Litinin, 16 ga Disamban 2024
An ji ƙarar jiniya a fadin birnin Tel Aviv da ma garuruwa da dama a tsakiyar Isra'ila.
Daga bisani sojojin Isra'ila sun ce jiniyar ta yi ta kuwwa ne sakamakon wani harin makamin roka da aka harba daga kasar Yemen, wanda aka daƙile kafin ya isa sararin samaniyar Isra'ila.
A cewar tashar ta Isra'ila ta Channel 14, lamarin ya shafi wasu 'yan kama wuri zauna a lokacin da suke kokarin tserewa.
2052 GMT — Akwai ƙananan yara cikin mutum 15 da Isra'ila ta kashe a harin da ta kai wata makaranta a Gaza
Akalla Falasdinawa 15 da suka hada da kananan yara ne suka mutu, yayin da wasu da dama suka jikkata, a wani harin da Isra'ila ta kai kan wani matsuguni da ke Khan Younis a kudancin Gaza a yammacin Lahadi, a cewar wata majiyar kiwon lafiya.
Shaidu sun ba da rahoton cewa, an kai harin ne a makarantar Ahmed Abdel Aziz, inda daruruwan fararen hula da suka rasa matsugunansu suka nemi mafaka.
Hukumar tsaron kiyaye farar hula ta Gaza ta tabbatar da harin, inda ta ce tawagogin likitocin sun gano gawarwaki da dama. Sai dai har yanzu ba a fayyace adadin yaran da abin ya shafa ba.
2039 GMT — Trump da Netanyahu sun tattauna kan batun fursunonin yaƙin Gaza da batun Syria
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya tattauna da zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald Trump game da halin da ake ciki a Syria da kuma ƙoƙarin da ake yi a halin yanzu na sakin waɗanda ake riƙe da su a Gaza, kamar yadda ya bayyana a ranar Lahadi.
Netanyahu ya ce ya tattauna da Trump a ranar Asabar da dare game da wannan lamarin.
Sai dai wani mai magana da yawun Trump ɗin a ranar Lahadi ya ƙi amincewa ya yi ƙarin bayani game da lamarin.