Alejandro Toledo, mai shekaru 78, ya shugabanci Peru daga 201 zuwa 2006. / Photo: AP

A ranar Litinin ɗin nan aka yanke wa tsohon shugaban kasar Peru Alejandro Toledo, hukuncin daurin shekara 20 da wata shida a kurkuku sakamakon samun sa da hannu a ayyukan ta'annati a kamfanin gine-gine na Barazil, Odebrecht, wanda ya yi shuhura wajen bayar da miliyoyin daloli na cin hanci ga jami'an gwamnati a Latin Amurka.

Mahukunta sun zargi Toledo da karbar dala miliyan 35 a matsayin cin hanci daga Odebrecht don bai wa kamfanin kwangilar babbar hanya a kasar da ke Amurka ta Kudu.

Babbar Kotun Kasar Da Ta Ƙware Kan Hukunta Manyan Laifuka da ke babban birnin Lima, ta tabbatar da hukuncin bayan tsawon shekaru ana ja-in-jar shari'a, ciki har da takaddamar ko za a ɗauko Toledo, da ya shugabanci Peru tsakanin 2001 da 2006 daga Amurka zuwa gida.

Mai Shari'a Ines Rojas ta ce wadanda Toledo ya ha'inta 'yan kasar Peru ne da suka amince masa a matsayin shugaban kasarsu.

Rojas ta kara da cewa a wannan matsayi, Toledo ne "ke da alhakin kula da lalitar talaka" kuma ke da alhakin "tabattar da an yi amfani da kudade ta yadda ya dace", amma maimakon haka sai "ya damfari kasar".

Kamfanin ya yi ikirarin sayen kwangiloli

Ta kara da cewa Toledo "yana da alhakin yin aiki da gaskiya da karewa da tsare dukiyar kasa da nisantar ɓarna da sata," amma bai yi hakan ba.

Odebrecht, wanda ya gina wasu manyan kayan more rayuwa a Latin Amurka, ya furta wa mahukuntan Amurka a 2016 cewa yana samun kwangila a kasashen nahiyar da dama ta hanyar bayar da cin hanci.

Binciken da Ma'aikatar Shari'a ta Amurka ta gudanar a kasashe sun haɗa da suka hada da Mexico, Guatemala da Ecuador.

A Peru, mahukunta sun zargi Toledo da wasu tsofaffin shugabannin kasa uku da karbar cin hanci daga hannun babban kamfanin gine-ginen.

Sun zargi Toledo da karbar dala miliyan 35 daga Odebrencht don bayar da kwangilar hanya mai nisan kilomita 650 da ta hada Barazil da kudancin Peru.

Toledo ya musanta zarge-zargen

Da fari an ayyana cewa wani bangare na hanyar zai lashe dala miliyan 507, amma a karshe sai da Peru ta biya dala biliyan 1.25.

A wasu gabobin, Rojas ta karanto wani bangare na shaidar da tsohon shugaban zartarwa na Odbrenchet a Peru, Jeorge Barta ya bayar, wanda ya fada wa masu gabatar da ƙara cewa tsohon shugaban ya kira shi har sau uku bayan barin aiki don neman a biya shi.

Toledo ya sunkuyar da kansa tare da kallon hannayensa, a yayin da Rojaske ke karanto bayanai a kotun.

Toledo ya musanta zarge-zargen da ake yi masa. Lauyansa, Roberto Siu, ya fada wa 'yan jarida cewa bayan samun wannan labari za su daukaka ƙara.

Tsohon shugaban kasar a ranar Litinin ya dinga yin yake, a wasu lokutan yana dariya, musamman a yayin da alkaliya ta ambaci miliyoyin daloli da suka shafi shari'ar da lokacin da take kokarin karanto jawabi daga takardun da ke gabanta a matsayin shaidar hukuncin da za ta yanke na karshe.

Ciwon daji

Sabanin haka kuma, a makon da ya gabata, ya bukaci kotu da murya mai rauni hannayensa ɗaure da ankwa, kamar yana rokon su bar shi ya koma gida saboda shekarunsa da ciwon daji da matslolin zuciya.

An fara kama Toledo mai shekaru 78 a wani gida da ke California a Amurka a 2019, inda yake zaune tun 2016, lokacin da ya dawo Jami'ar Stanford, tsohuwar makarantar da ya yi, a matsayin malamin nazarin Ilimi a Latin Amurka.

An fara tsare shi a kurkukun San Francisco, amma an sake shi tare da yi masa talala a 2020 saboda annobar Covid-19 da kuma tabarbarewar lafiyarsa.

A 2022 kuma an mayar da shi zuwa Peru bayan kotun daukaka ƙara ta ƙi amincewa da neman kar a dawo da su.

Hukunci kotu mai tarihi

Tun wannan lokacin ake tsare da shi tare da sanya idanu a kansa.

Rojas ta kuma ce Toledo zai fara aiki da wa'adin ne daga watan Afrilun 2023. Kuma zai yi zaman sauran shekarun da suka rage masa a wani kurkuku da ke wajen babban birnin Lima da aka gina musamman don tsofaffin shugabannin kasar Peru.

Mai gabatar da kara Jose Domingo Perez bayan jin shari'ar, ya bayyana hukuncin da 'na tarihi' kuma ya ce hakan na nuni da jama'ar Peru na hukunta ayyukan cin hanci da rashawa.

TRT Afrika