Hukumomi a Amurka sun kama ‘yan ci-rani 538 da kuma mayar da ɗaruruwa ƙasashensu kwanaki kaɗan bayan sabon shugaban ƙasar Donald Trump ya kama aiki.
Sakatariyar watsa labaransa Karoline Leavitt ce ta tabbatar da batun kamen da korar ɗaruruwan mutane a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X .
“Gwamnatin Trump ta kama ‘yan ci-rani da ke zaune ba bisa ƙa’ida ba 538,” kamar yadda Karoline Leavitt ta bayyana a shafinta na X inda ta ƙara da cewa an fitar da “ɗaruruwa” cikin jirgin soji.
“Kora mafi girma a tarihin Amurka na kan hanya. Kyawun alƙawari cikawa,” kamar yadda ta bayyana.
Trump ya yi alƙawari a kan yin dirar mikiya kan waɗanda suka shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba a yayin yaƙin neman zaɓen ƙasar tare da soma jawabinsa na farko bayan kama aiki da sanar da wasu sabbin dokoki, ciki har da batun korar baƙi da yin garambawul ga ɓangaren hanyoyin shiga cikin Amurka.
Trump ya sha alwashin yin kora mafi girma a tarihin Amurka inda ya lashi tokobin korar kimanin ‘yan ci-rani miliyan 11 da ke zaune a Amurka ba tare da izini ba.
A ranar farko da ya hau kan karagar mulki, ya rattaba hannu ayyana kan dokar ta-baci a iyakar Amurka da ke kudancin ƙasar kuma ya sanar da tura ƙarin sojoji zuwa yankin yayin da ya sha alwashin korar “baƙi masu aikata laifuka.”