Shugaban Amurka ya ce  wanda ya ce mana kule, za mu masa cas./Hoto: Reuters

Rundunar sojin Amurka ta ce dakarunta sun kaddamar da jerin hare-hare ta sama a wasu yankuna na Syria da Iraki domin yin ramuwar gayya kan kisan sojojinsu uku da aka yi a wani sansanin sojin Amurka da ke kan iyakar Jordan da Syria.

Dakarun sojojin Amurka sun kai hare-hare kan runduna ta musamman ta Revolutionary Guards ta Ira da kuma kungiyoyin masu tayar da kayar baya da ke da Tehran inda hare-haren suka sauka a fiye da yankuna 85 a Iraki da Syria, a cewar rundunar ranar Juma'a.

"An kai hare-haren na sama ne da makamai fiye da 125 da ke iya sauka a wurin da aka cilla su ba tare da kuskure ba," a cewar Rundunar da ke bayar da umarni ta sojojin Amurka a wani sako da ta wallafa a soshiyal midiya.

Ta kara da cewa an kai hare-haren ne a cibiyoyin bayar da umarnin soji da na leken asiri da rokoki da makamai masu linzami da wuraren ajiye jirage marasa matuka na masu tayar da kayar baya da kuma dakarun tsaron Iran "wadanda suke taimaka wa wurin kai hare-hare kan Amurka da kawayenta."

Shugaba Joe Biden ya jaddada cewa Amurka za ta kara kaimi wurin mayar da martani. "Mun soma mayar da martani yau kuma za mu kara kaimi wurin yin hakan a wurare da lokutan da muka sanya wa ido," in ji Biden.

"Duk da yake Amurka ba ta tsokanar fada a Gabas ta Tsakia da wasu yankuna, ina so na bayyana karara cewa duk wanda ya ce mana kule, za mu masa cas," a cewar shugaban Amurka.

Jami'an gwamnatin Iraki sun yi tir da wadannan hare-hare a kan iyakokinsu, suna masu cewa hakan ya keta alfarmarsu ta kasancewa kasa mai cin gashin kanta sannan za su nuna fushinsu mai girma.

Janar Yehia Rasool, kakakin Firaiminista Mohamed Shia al Sudani, ya yi gargadi cewa harin da aka kai a yammacin Iraki, kusa da kan iyaka da Syria, zai iya jefa yankin cikin hatsari.

TRT World