Amurka na goyon bayan bayar da kujerun din-din-din a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ga ƙasashen Afirka biyu, da kujera ɗaya ta karɓa-karɓa ga ƙasashen dake ƙananan tsibirai, kamar yadda Jakadiyar Amurka a MDD Linda Thomas-Greenfield za ta bayyana a ranar Alhams ɗin nan.
Thomas-Greenfield ta faɗa wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa tana fatan sanarwar za ta "kara ƙarfafa wannan manufa ta hanyar da za a iya kawo sauyi a Kwamitin Tsaro a nan gaba," inda ta kuma ce wannan na daga manufofin Shugaba Joe Biden.
Ƙasashe masu tasowa sun jima suna neman a ba su kujerun din-din-din a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya, kwamiti mafi ƙarfi a Majalisar. Amma bayan shekaru ana tattaunawa kan yin sauye-sauye, an kasa cimma matsaya kuma ba a da tabbacin ko goyon bayan Amurka na iya ya janyo ɗaukar wannan mataki ba.
Kafin bayar da sanarwar a Kwamitin Harkokin Kasashen Waje a New York a ranar Alhamis, Thomas Greenfield ta yi karin haske ga Reuters cewa Washington ba ta goyon bayan ƙara yawan kasashen da suke da karfin zartar da hukunci na hawa kujerar na-ƙi sama da biyar a suke da shi a yanzu.
Kwamitin Tsaron na da alhakin samar da tsaro da zaman lafiya a duniya, kuma yana da karfin saka takunkumai da hana saye ko mallakar makamai, kuma yana bayar da umarnin amfani da ƙarfi.
A lokacin da aka kafa Majalisar Ɗinkin Duniya a 1945, Kwamitin Tsaro na Majalisar na da mambobi 11. An kara yawan su zuwa 15 a shekarar 1965, 10 zaɓaɓɓu dake karba-karba na shekru biyu-biyu, da guda biyar da ke da karfin zartar da ikon hawa kujerar na-ƙi; Rasha da China da Faransa daAmurka da kuma Birtaniya.
Batun halasci
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres na goyon bayan kawo sauyi a Kwamitin Tsaron.
"Kana da Kwamitin Tsaro da ya samu kansa a irin halin da aka shiga bayan Yaƙin Duniya na Biyu... wannan na da matsalar halasci, wannan na da matsalar tasiri, yana bukatar yi masa sauye-sauye," kamar yadda Guterres ya faɗa wa Reuters a ranar Laraba.
Ana yin duk wani sauyi na zama mamba a Kwamitin Tsaro ta hanyar kwaskwarima ga dokar da ta kafa Majalisar Dinkin Duniya. Wannan na buƙatar amincewar kashi biyu cikin uku na Babban Zauren Majalisar, ciki har da mambobin din-din-din masu hawa kujerar na-ƙi su biyar.
A cikin sama da shekaru 10 Babban Zauren MDD da ke da mambobi 193 kowace shekara na tattaunawa kan kawo sauyi da yin gyara a Kwamitin Tsaron.
Amma a shekarun baya-bayan nan an yi ta samun ɗaga murya daga ƙasashe saboda yadda ƙasashen da suke adawa da juna suke cin karo kan wasu batutuwa, musamman da a yanzu ƙasar da ke da karfin hawa kujerar na-ƙi Rasha ta kai hari Ukraine.
Thomas-Greenfield za ta bayyana a ranar Alhamis cewa,"Mafi yawan tattaunawa kan sauye-sauye a Kwamitin Tsaro na karewa ne a baka kawai," kamar yadda Reuters ta gani a jawabin da aka tanada za ta yi, wanda zai bayyana goyon bayan Washington ga fara tattaunawa kan rubuta wani daftari na gyara kan dokar da ta kafa majalisar, don a ƙara yawan kasashe a Kwamitin.
Thomas Greenfield ta faɗa wa Reuters cewa ba za ta iya cewa ga lokacin da za a ɗauka ba kafin Babban Zauren ya amince da wannan mataki.
A kowacce shekara Babban Zauren MDD yana zaɓar sabbin mambobi biyar daga nahiyoyi daban-daban a matsayin mambobin shekaru biyu a Kwamitin Tsaro na MDD. A yanzu Afirka na da kujeru uku na karɓa-karɓa tsakanin ƙasashen nahiyar.
"Matsalar ita ce, waɗannan ƙasashe mambobin din-din-din ba sa bai wa kasashen Afirka sukunin bayar da cikakkiyar damar amfana da ilimi da muryoyinsu a ayyukan Kwamitin ... a koyaushe su jagoranci warware matsalolin da ke damun mu gaba ɗaya - waɗanda kuma ke damun wasu yankunan na Afirka," Thomas-Greenfield za ta bayyana a wajabinta.
Za kuma ta bayyana cewa ƙasashen kananan tsibirai sun cancanci zama mambobin da za su dinga yin karɓa-karɓa saboda suna bayar da "kyawawan shawarwari kan batutuwan tsaro da zaman lafiyar duniya, ciki har da tasirin sauyin yanayi."