An gudanar da "Taron kan dangantaka tsakanin Turkiyya da Birtaniya," wanda Ma'aikatar Sadarwar Turkiyya ta karɓi baƙuncinsa a Ofishin Jakadancin ƙasar da ke London, wanda ya samu halartar malaman jami'a da ƴan jarida da masana da ƴan kasuwa.
Taron ya mayar da hankali kan sauye-sauyen da aka samu game da dangantaka tsakanin Turkiyya da Birtaniya bayan ficewarta daga Tarayyar Turai, wato Brexit da sauran mu'amala tsakanin ƙasashen biyu.
Da yake jawabi ga mahalarta taron ta manhajar bidiyo, Daraktan Sadanarwa na Fadar shugaban ƙasar Turkiyya Fahrettin Altun ya jaddada ƙalubalen da ke fuskantar duniya a wannan lokaci, ciki har da rikice-rikice na yankuna da ma na duniya baki ɗaya.
Altun ya yi tsokaci kan rikicin Ukraine da Rasha inda ya ce ya kamata a riƙa kai zuciya nesa, yana mai yin kira a tattauna domin kawo ƙarshensa maimakon ci gaba da yaƙi. Kazalika ya fito da mummunan tasirin yaƙin kan ƙasashen duniya, alal misali, matsalar ƙarancin abinci, wanda Turkiyya ta taimaka wurin kawarwa inda ta sa baki aka ƙulla yarjejeniyar fitar da hatsi.
Haka kuma Altun ya jaddada suka kan yaƙin da Isra'ila take yi a Falasɗinu, da musgunawar da take yi wa mazauna yankin inda take amfani da yunwa a matsayin makamin yaƙi. Ya nuna damuwa kan yadda ake samun ƙaruwar wariyar launin fata da ƙyamar Muslmai, musamman a ƙasashen Yammacin duniya.
Altun ya kuma jaddada matsayin Turkiyya wajen yaƙi da masu nuna wariyar launin fata, yana mai bayyana matakan Turkiyya na magance matsalar ƴan ci-rani.
Da yake tsokaci kan illolin labaran ƙarya, Altun ya ce suna jawo rashin jituwa da cutarwa a cikin al'umma, yana mai bayyana cewa magance wannan matsala a ƙasar da ma ƙasashen duniya yana da matuƙar muhimmanci. Ya jaddada muhimmancin kare mutuncin Falasɗinawa, yana mai cewa hakan tamkar kare mutuncin ɗan'adam ne.