Talata, 15 ga watan Oktoba, 2024
1511 GMT –– Ma'aikatar Lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa mutum 41 ne suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai ranar Litinin.
1313 GMT –– Turkiyya ta buƙaci da a ƙaƙaba wa Isra'ila takunkumi saboda zubar da jinin da take yi a Gaza
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya yi kira da a ƙaƙaba wa Isra’ila takunkumi, yana mai kira ga ƙasashen duniya da su yanke duk wani goyon baya da suke bayarwa kan rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.
Ministan Harkokin Wajen kasar Hakan Fidan ya fadi hakan ne a bayanin da ya yi wa wakilan jam'iyya mai mulki a wani taro game da kasar Falasdinu, inda ya kara da cewa: "Mun kai iyakar kalamai, diflomasiyya da siyasar kasa da kasa. Dole ne mu fara da saka mata takunkumi."
1115 GMT –– Isra'ila ta kashe aƙalla mutum 50 a Gaza kuma tankokin yaƙinsu sun sake kutsawa arewacin yankin
Sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa aƙalla 50 a fadin Gaza yayin da sojojin Isra’ila suka ƙara kutsawa can ciki kusa da Jabalia da ke arewacin yankin.
Jami'an kiwon lafiya na Falasdinawa sun ce aƙalla mutum 17 ne suka mutu sakamakon gobarar da Isra'ila ta haddasa a kusa da Al Falouja a Jabalia, mafi girma daga cikin sansanonin 'yan gudun hijira takwas masu tarihi a Gaza, yayin da wasu 10 suka mutu a Bani Suhaila da ke gabashin Khan Younis a kudancin kasar a lokacin da wani makami mai linzami da Isra'ila ta jefa ya fada wani gida.
Tun da farko a ranar Talata, wani harin da jiragen yakin Isra’ila suka kai ya lalata gidaje uku a yankin Sabra da ke wajen birnin Gaza, kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta yankin ta ce ta gano gawarwaki biyu daga wurin, yayin da ake ci gaba da neman wasu mutum 12 da ake kyautata zaton suna cikin gidan a lokacin kai harin.
An kashe wasu mutum takwas a lokacin da aka kai hari wani gida a sansanin Nuseirat da ke tsakiyar Gaza.
Daga baya a ranar Talata, ma'aikatar lafiya ta Gaza ta ce likita daya ya mutu a lokacin da ya yi kokarin taimaka wa mutanen da suka jikkata a harin da Isra'ila ta kai a Al Falouja a Jabalia.
Ya kara da cewa ma'aikatan jinya da dama sun samu raunuka a lokacin da Isra'ila ta yi ruwan wuta a kan motar daukar marasa lafiya a arewaci da kudancin Gaza
0634 GMT — Sabbin hare-haren da Isra'ila ta kai a Gaza sun kashe Falasɗinawa aƙalla 29
Sabbin hare-haren da Isra'ila ta kai a sassa daban-daban na Gaza sun kashe Falasɗinawa aƙalla 29, ciki har da mata da yara, a cewar jami'an kiwon lafiyar Falasɗinu.
Majiyoyi sun ce dakarun Isra'ila sun kai hari a yankuna da dama da suka haɗa da Khan Younis, sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat da na Jabalia.
Isra'ila ta kashe Falasɗinawa fiye da 42,000 a yaƙin da take yi a Gaza, a cewar hukumomin kiwon lafiyar yankin, galibinsu mata da yara.
Yaƙin ya lalata yawancin yankin Gaza tare da korar kusan kashi 90 cikin ɗari na mutanen yankin su miliyan 2.3.
2241 GMT —An ɓoye Netanyahu a wani wuri don tsoron hari daga Hezbollah
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya tabbatar wa Amurka cewa dakarunsa za su kai hari kan cibiyoyin sojojin Iran, ba tashar makamashin nukiliya ko rijiyoyin man fetur ba bayan da Shugaba Joe Biden ya gargaɗe shi game da kai hari kan tashar ta nukiliya, a cewar wasu rahotanni.
Jami'ai biyu da ba sa so a ambace su, ciki har da wani jami'in Amurka, sun ce Netanyahu ya tabbatar da cewa zai kai hari kan cibiyoyin sojin Iran a wata tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da Biden a makon jiya, a cewar jaridar The Washington Post.
2113 GMT — An ɓoye Firaministan Isra'ila Netanyahu a wani wuri mai tsaro a asibiti bayan an ji ƙarar jiniya
An garzaya da Firaminista Benjamin Netanyahu wani wuri mai cikakken tsaro a cikin asibiti da ke arewacin Isra'ila bayan an ji ƙarar jiniya da ke nuna yiwuwar kai masa harin roka daga Lebanon ranar Lahadi.
Lokacin da jiniyar ta yi ƙara, Netanyahu yana Asibitin Hillel Yaffe da ke birnin Hadera, inda ya ziyarci sojojin Isra'ila da suka jikkata sakamakon harin jirgi mara matuƙi da ƙungiyar Hezbollah ta kai musu inda ta kashe huɗu daga cikinsu tare da jikkata gommai, a cewar kafar watsa labaran gwamnatin Isra'ila KAN.
Bayan jin ƙarar jiniyar, jami'an tsaron da ke tare da Netanyahu sun ɗauke shi zuwa wani wuri mai cikakken tsaro da ke cikin asibitin, in ji KAN.