A yanzu Falasɗinawa na ɓuya a tsohon gidan yari saboda babu sauran mafaka a Gaza / Hoto: AA / Photo: Reuters Archive

Juma'a, 26 Yuli, 2024

1403 GMT A yanzu Falasɗinawa na ɓuya a tsohon gidan yari saboda babu sauran mafaka a Gaza

Bayan da Isra'ila ta kwashe makonni tana kai musu hari babu inda za su je, ɗaruruwan Falasdinawa sun koma ɓuya a wani tsohon gidan yarin Gaza da aka gina domin tsare masu laifin kisan kai da ɓarayi.

Yasmeen al-Dardasi ta ce ita da 'yan'uwanta suna ji suna gani suka dinga wuce wasu mutanen da suka samu raunuka da ba za su iya taimaka musu ba yayin da suke ƙaura daga wasu yankuna da ke kudancin birnin Khan Younis zuwa gidan yarin.

Sun yini a karkashin bishiya kafin su wuce zuwa tsohon gidan yarin, inda yanzu suke zaune a ɗan ƙaramin masallacin da ke wajen. Suna samun kariya daga zafin rana, amma babu sauran jin daɗi.

Mijin Dardasi yana fama da ciwon ƙodar da huhu, amma babu katifa ko bargo. "Mu ma ba mu zauna a nan ba," in ji Dardasi, wadda kamar sauran Falasdinawan tana fargabar yaƙi ya sake cim mata.

1354 GMT — 'Yan sandan Isra'ila sun hana daruruwan Musulmai sallah a Masallacin Ƙudus

‘Yan sandan Isra’ila sun hana ɗaruruwan matasan Falasdinawa shiga Masallacin Ƙudus da ke Birnin Kudus domin yin Sallar Juma’a, kamar yadda shaidu suka shaida wa Anadolu.

Jami’an ‘yan sandan da aka girke a kofar masallacin sun hana ɗaruruwan matasa da suka je yin sallah, kamar yadda shaidun suka ce, kuma ‘yan sandan sun far wa wasu daga cikin su.

Wadanda suka shaida lamarin sun ce ‘yan sandan sun lakaɗa wa wani matashin duka a kusa da kofar Zaki, inda har ya ji rauni a kansa. Har ila yau, sun ce 'yan sanda sun kai wa wani ma'aikacin gidan talabijin na Turkiyya TRT hari a yankin ba tare da wani dalili ba.

Rundunar ‘yan sandan Isra’ila ba ta bayar da dalilan hana dimbin matasan shiga masallacin ba ko kuma dalilin kai hare-haren. Sai dai an tsaurara matakan hana matasa shiga masallacin a 'yan makonnin da suka gabata.

1158 GMT — Hukumar Kula da Falasɗinawa 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNRWA) ta ce an tilasta wa Falasɗinawa tara daga cikin 10 barin gidajensu a Gaza.

A wata sanarwa da ta fitar, hukumar ta ce: "An tilasta wa Falasɗinawa 9 daga cikin 10 barin gidajensu a Gaza."

Ta ƙara da cewa "iyalai suna neman mafaka a inda za su iya samu: a makarantun da ke cike da jama'a, da gine-ginen da aka rusa, da tantuna da bola."

Hukumar ta ce "dukkan waɗannan wurare ba su da aminci. Yanzu mutane ba su da inda za su iya tsugunawa."

2300 GMT — Wani shugaban Falasɗinawa da ke da alaƙa da Hamas a Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye ya mutu a hannun Isra’ila sakamakon tsananin rashin lafiya, a cewar wata ƙungiyar gwamnati ta Falasɗinu.

Mustafa Muhammad Abu Ara, mai shekaru 63, ya rasu ne bayan da aka kai shi asibiti daga gidan yarin Ramon da ke kudancin Isra'ila, in ji wata sanarwa da hukumar kula da fursunonin Falasɗinu ta fitar.

"Kafin a kama shi, yana fama da rashin lafiya mai tsanani da ke buƙatar kulawa sosai, amma tun daga lokacin da aka kama shi, Sheikh Abu Ara, kamar sauran fursunoni, yake fuskantar wulaƙancin da ba a taɓa ganin irinsa ba tun farkon yaƙin.''

2222 GMT — Hamas ta yi Allah wadai da azabtar da Falasɗinawa 6 da Isra'ila ta yi a gidajen yarinta

Ƙungiyar Hamas ta yi Allah wadai da azabtar da Falasɗinawa shida waɗanda suka haɗa da mata biyu da aka sako daga gidajen yarin Isra'ila.

A wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar gwagwarmaya ta Falasɗinu ta bayar da misali da shaidar da ta samu daga wurin fursunonin da aka sako wadda kamfanin dillancin Labarai na Anadolu ya tattaro.

Falasɗinawa sun bayyana cewa sun fuskanci "mummunar azabtarwa da duka a tsawon lokacin da suke tsare."

Hamas ta ce azabtarwar da aka yi musu "tana nuna yanayin da dubban fursunoni da sauran Falasɗinawan da aka tsare suke fuskanta a mamayar Isra'ila da kuma hukunci a cibiyoyin tsarewa irin salon 'yan Nazi."

Kazalika ƙungiyar ta jaddada cewa irin wannan azabtarwa, ''waɗanda ba su da imani da tausayi da sanin ƙima da darajar ɗan'adam ne suke aiwatar wa a kan mutane masu rauni da ba su ji ba ba su gani ba.''

Ta ce fursunonin da aka sako "sun nuna alamun rashin lafiya saboda azaba da sakaci da yunwa da zagi da kuma rashin barci da suka fuskanta," tana mai ƙira kan a gaggauta daukar mataki mai tsauri don fallasa abubuwan da ke faruwa a gidajen yarin Isra'ila da kuma ceto dubban Falasdinawa da ake tsare da su a wannan wuri- da ake aiwatar da salon tsarewa irin na Nazi.''

'Yan uwan ​​Falasdinawan da suka rasa rayukansu a harin da Isra'ila ta kai, sun shiga yanayin alhini yayin da ake ɗaukar gawawwaki daga dakin ajiye gawa na Asibitin Nasser domin binne su a maƙabartar Khan Yunis / Hoto: AA  

0036 GMT — Falasɗinawa da Yahudawa sun gudanar da zanga-zangar lumana

Ɗaruruwan Falasɗinawa da Yahudawa na Isra'ila ne suka yi ta rera taken "E, a samu zaman lafiya, e, ga yarjejeniya", a yayin wani tattaki da suka yi a birnin Tel Aviv, suna masu neman a kawo ƙarshen kashe-kashe da ake yi a Gaza.

Masu zanga-zangar sun ce ajandarsu ta farko ita ce a tsagaita wuta a yankin da aka mamaye, amma gaba ɗaya suna so a sake maido da dangantakar Falasɗinu da Isra'ila tare da ba da damar kafa sabuwar rayuwa.

2044 GMT — Masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinu sun yi zaman dirshan a kusa da Fadar White House

Masu zanga-zangar adawa da kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Gaza da aka yi wa ƙawanya, sun gudanar da 'zaman dirshan' a tsallaken wurin shaƙatawa na Lafayette da kuma Fadar White House a yayin ganawar Shugaba Joe Biden da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.

Masu zanga-zangar sun zuba jan ruwa a kan titi, suna masu cewa hakan na nuni da jinin waɗanda aka kashe a Gaza.

Kazalika sun yi ta rera taken "A kama Netanyahu" tare da nuna hoton Firaministan sanye da wata riga mai launin ruwan lemu da ke da jini, kana an yi rubutu a kai da ke cewa "A kama shi da laifin take hakkin ɗan'adam."

TRT Afrika da abokan hulda