A shekarar da ta gabata an baje-kolin Bayraktar Kizilelma/ Photo: AA

A yayin kasuwar baje-kolin kayan fasahar kere-kere da sufurin jiragen sama mafi girma a Türkiye, za a baje-kolin jirgin saman yaki mara matuki mai dauke da makamai samfurin Bayraktar TB3 wanda kamfanin Baykar na kasar ya samar.

Za a gudanar da baje-kolin a filin tashi da saukar jiragen saman Ataturk da ke Istanbul daga 27 ga Afrilu zuwa 1 ga Mayun 2023.

A wannan shekarar za a fara gwajin tashin jirgin mara matuki mai dauke da makamai da kan iya tashi da sauka a kan manyan jiragen yaki da ke da karamin filin jirgi. Za a gwada tashin jirgin kan jirgin ruwan yaki na Turkiye mai suna TCG Anadolu.

Jirgin mara matuki na da karfin yin layar zana ga wadanda ke kula da shi daga nesa.

An gudanar da bukin Teknofest na shekarar da ta gabata a garin Samsun da ke yankin tekun Bahar Maliya na Turkiye.

A yayin bukin an baje-kolin jirgin saman yaki mara matuki samfurin Bayraktar Kizilelma.