Turkiyya na kara yin fice a duniya wajen samar da kayan tsaro na zamani. Hoto. AA

A ranar 25 ga Yuli aka fara baje-kolin kayan tsaro ta kasa da kasa mai taken ‘IDEF'23 International Defense Industry Fair’ wanda aka shirya gudanarwa a watan Mayu amma saboda zabukan Turkiyya aka dage zuwa tsakanin 25 da 28 ga watan Yulin 2023.

Baje-kolin da e da matsayi na hudu mafi girma a duniya, zai samu halartar manyan kamfanoni da kayayyakinsu mafiya girma daga kasashe daban-daban.

Ma’aikatar Tsaron Turkiyya ce ke karbar bakuncin baje-kolin kayan tsaron da Asusun Rundunar Sojin Saman Turkiyya ya shirya, inda za a nuna wa duniya kayan tsaro na cikin gida da na waje a Baban Filin Taro na Cibiyar TUYAP.

A yayin baje-kolin da aka gabatar ta karshe ta IDEF’21, an samu halarta kamfanoni 1,200 daga Turkiyya da sauran kasashen duniya.

An kafa tantuna 1,238 don nuna kayayyakin tsaro daga kasashe 53, yayin da mutum 68,795 daga kasashen duniya 94 suka ziyarci baje-kolin.

A wannan karon, muhimman kayan tsaro na zamani da masana’antun tsaron Turkiyya suka samar za su zama a kan gaba a wajen baje-kolin.

Kamfanin Aselsan, daya daga cikin manyan kamfanonin tsaro na Turkiyya zai baje-kolin garkuwar makamai masu linzami samfurin GOKSUR da kuma makamin tafi da gidanka na GOKBERK.

Baje-kolin sabbin kayan tsaro da aka samar a Turkiyya

Kasancewar sa a kan gaba wannan baje-koli, Aselsan ya samar da GOKSUR da kakkarfan tsarin kalubalntar jiragen yaki marasa masu matuka da masu matuka, jiragen yaki masu saukar ungulu da makamai masu linzami na kasa da na ruwa.

Wani sabon abu da Aselsan zai baje-koli a wajen shi ne GOKBERK, wani tsarin harba makami ne na tafi da gidanka, aaboda fasahar da aka yi amfani da ita wajen samar da shi, na iya cimma burins aba tare da layin hakaito manufa ba.

Aselsan ya samar da ERAL da dakrun sojin saman Turkiyya za su fara amfani da shi. Hoto: AA

ERALP da aka samar da cigaban bukatar Rundunar Sojin Saman Turkiyya, na’urar radar mai hangen nesa ta Turkiyya, za ta sadu da maziyarta baje-kolin. Tana da ikon hango jirage tun daga nesa sosai ta hanyar amfani da algorithm.

A baje-kolin da ya gabata, kamfanin da gwamnati ke kula da shi ya nuna wa duniya ENGEREK-2 da ASELFLIR-500, wasu garkuwar makamai masu linzami da jiragen sama da rundunar sojin ruwa ke amfani da su.

Sauran kamfanonin tsaro na Turkiyya ma sun gabatar da nasu kayayyakin a kasuwar baje-kolin, kayan tsaron teku da na sama.

Baje-kolin kayan tsaro na kasashen waje

Bayan ga kayan tsaron da aka samar a cikin gida Turkiyya, IDEF’23 na kuma gabatar da kayayyakin da aka samar a kasashen duniya daban-daban.

Hadaddiyar Daular Larabawa na daya daga cikin wadannan kasashe, kamfanin ‘Emirates Defense Companies Council (EDCC)’ zai jagoranci rumfar baje-kolin kayan da kasar ta samar a wajen IDEF’23.

Halartar Hadaddiyar Daular Larabawa baje-kolin wani bangare ne na hadin kai a fannin tsaro da Turkiyya da kasar ke yi.

Anas Naser Al Otaiba, Janaral Manaja na EDCC ya bayyana cewa “Halartar EDCC zuwa IDEF’23 na bayyana irin karfin hadin kai da girmamar alakar da ke tsakanin Hadaddiyar Daular Larabawa da Turkiyya, karkashin shugabanci Mai Girma Sarki Shaikh Shugaban Kasa Mohammed bin Zayed Al Nahyan da Mai Girma Shugaba Recep Tayyip Erdogan.”

Kokarin da ake yi na hada kai a fannonin cigaba na daga cikin yarjejeniyar Habaka Cigaban Tattalin Arziki Mai Fadi da Hadddiyar Daular Larabawa da Tukiyya suka sanya hannu a kai a watan Maris din 2023.

Ana sa ran halartar waakilan China a baje-kolin, inda kamfaninda yafi kowanne fitar da jiragen yaki marasa matuka a duniya tare da wasu kamfanunnuka saba’in da hudu za su halarci wajen.

Rawar Turkiyya wajen samar da kayan tsaro a duniya

Kasancewar samun mahalarta da masu baje-kolin kayayyakinsu da suka samar a baya-bayan nan musamman a masana’antar tsaro ta Turkiyya, baje-kolin IDEF’23 na bayyana rawar da Turkiyya ke taka wa a fannin samar da kayan tsaro a duniya.

A farkon makon da ya gabata, Saudiyya da Turkiyya sun sanya hannu kan kai jirgin yaki mara matuki na Bayraktar AKINCI zuwa Saudiyya, a yayin ziyarar da Shugaba Erdogan ya kai kasashen yankin Gulf.

Yarjejeniya ta zama mafi girma a tarihin Turkiyya, ta hada da musayar fasahar kere-kere da samar da kayayyaki tsakanin kasashen biyu.

Madalla da nasarar AKINCI a yakin Rasha da Yukren da kuma yakin Nagorno-Karabakh, kasashen duniya na ci gaba da nuna sha’awar sayen kayan kamfanin Baykar.

Kudaden shigar da masnaa’antar tsaron Turkiyya ke samu sun karu zuwa dala biliyan 4.3 a 2022, daga dala biliyan 3.2 a 2021, kamar yadda alkaluman da Hukumar Fitar da Kayayyaki ta Turkiyya ta fitar suka bayyana.

Sashn tsare da samar da kayan tsaro na sama ne suka zama na biyu a duniya a shekarar wajen fitar da kayayyaki zuwa kasashen ketare.

Baje-kolin zai zama dandalin bayyana dukkan ci-gaban fannin samar da kayan tsaro ba iya na Turkiyya ba, har ma da na sauran kasashen duniya da suke halartar baje-kolin, wanda hakan zai iya bayar da damar hada kai don musayar damarmaki da fasahar kere-kare.

TRT World