Turkiyya ta kammala kera jirgin ruwan yaki da jiragen sama ke iya tashi da sauka a kansa

Turkiyya ta kammala kera jirgin ruwan yaki da jiragen sama ke iya tashi da sauka a kansa

An saka sanya hannu kan yarjejeniyar kera sabbin jiragen yaki uku da MILGEM domin amfanin Rundunar Sojin Turkiyya.
Turkiyya na samar da kayan tsaro manya da kanana domin daina dogaro da kasashen waje / Photo: AA

A mako mai zuwa za a mika wa Rundunar Sojin Ruwan Turkiyya jirgin ruwa na yaki TCG Anadolu da jiragen sama na yaki ke iya tashi da sauka a kansa wanda aka samar a kasar.

Shugaban Hukumar Kula da Masana’antun Kayan tsaro ta Turkiyya Ismail Demir ya sanar da cewa a ranar Litinin mai zuwa za a yi bikin mika jirgin ruwan na TCG Anadolu a Hedikwatar Rundunar Sojin Ruwa.

Demir ya kara da cewa suna da manufar shigar da jirgin yaki mara matuki na Bayraktar TB3 zuwa cikin jiragen za za su dinga sauka kan TCG Anadolu a wannan shekarar.

Ya ce, ana shirin yadda jirgin sama kirar Turkiyya samfurin Hurjet ma zai dinga sauka a kan TCG Anadolu.

Demir ya kara da cewa ya yi wuri a fara batun jirgin mara matuki na Anka=3 ya fara sauka a kan TCG Anadolu.

Jirgin ruwan yaki na TCG Anadolu da aka samar da cikakkiyar fasaha zai iya daukar rundunar mayaka da kayan aikinsu tare da kai su duk indn ake so a kan teku ba tare da samun wani taimako daga sansani ba.

TCG Anadolu zai zama babban mai bayar karfi ga Dakarun Ruwan Turkiyya, musamman ma yadda za a saka masa na’urar hangen nesa ta UCAV.

Jirgin na da tsayin mita 231 da fadin mita 32, sannan yana da nauyin tan dubu 27,000.

TRT World