Daga Charles Mgbolu
An bude baje-kolin fasaha na Turkiyya da jiragen sama da aka yi wa lakabi da TEKNOFEST 2023 zango na uku kuma na karshe a ranar Laraba a birnin İzmir da ke kudu maso yammacin kasar.
Bikin kwana biyar din za a kammala shi a ranar 1 ga watan Oktoba, kuma tawagar fasaha ta Turkiyya (T3) ce ta shirya shi da hadin gwiwar Ma'aikatar Masana'antu da Fasaha ta Turkiyya.
Abu ne mai daukar hankali yadda aka baje-kolin jiragen sama da fasaha da manhajoji da yin taruka kan fannin ilimi da sauransu.
Bikin baje-kolin bana ya zo ne a muhimmin lokacin da Turkiyya take bikin cika shekara 100 da kafuwa.
Bikin na bana an yi shi ne daki-daki, inda aka fara yin zangon farko a birnin Istanbul a watan Afrilu, wanda mutum miliyan biyu suka halarta – abin da ba a taba ganin irinsa a baya ba.
An yi zango na biyu ne a birnin Ankara tsakanin ranar 30 ga watan Agusta zuwa ranar 3 ga watan Satumba, a filin jirgin saman Etimesgut, inda mutum 943,000 suka halarta.
Birnin İzmir yanzu yana cike da farin ciki yayin da yake fatan kafa tarihi lokacin baje-kolin a sararin samaniyarsa.
Za a yi bikin ne a filin jirgin saman Çiğli a İzmir kuma za a baje-kolin fasaha da jiragen sama da motoci da yin taruka kan fannin ilimi da sauran abubuwa masu kayatarwa.