Jirgin yaki mara matuki kirar Turkiyya mai suna Anka ya shirya don fara hidimtawa wasu kasashen duniya, in ji wani jami’in kamfanin da ya samar da kayan.
“Kamfanin samar da kayan tsaron sama na Turkiyya TAI zai fitar da jirgin yaki mara matuki Anka zuwa Karin kasashe hudu” in ji shugaban samar da kayayyakin kamfanin Injiniya Ziya Dogan yayin tattaunawar su da kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
“Wata kasar waje da ta sayi jirgin na ci gaba da amfani da Anka,” in ji Dogan, inda ya kara da cewa an sanya hannu kan yarjejeniyar fitar da jirgin zuwa karin wata kasa a 2024.
Dogan ya kuma cewa Anka ya yi shawagi a sama na tsawon awanni 200,000 a hannun wadanda suka saye shi a cikin gida.
A shekarar 2010 ne Anka ya fara tashi sama.
Jirgin Anka na aiya aiki dare da rana kuma a kowanne irin yanayi, na iya samun abun da ya hara daidai, na iya gudanar da aikin liken asiri, na gabatar da tashi da sauka shi kadai cikin nasara.
Kamfanin TAI da ke Ankara na samar da da jiragen sama marasa matuka, jiragen yaki, jirage masu saukar ungulu da tauraron dan adam da ma kayayyakin gyara su.
An kafa kamfanin TAI a watan Yuni 1973, da manufar rage dogaron da Turkiyya ke yi kan kasashen waje waje.