Turkiyya na ci gaba da habaka masana'antar tsaron ta d atake tashe yau a duniya/ Hoto: TRT World

Hurjet, jirgin saman yakin gaya-wa-hazo-na-wuce da Turkiyya ta samar ya tashi a karon farko, in ji shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan a wani sako da ya wallafa a shafin Twitter.

Jirgin ya samu ne sakamakon manyan ayyukan samar da jiragen yaki da na bayar da horo wadanda Hukumar Sufurin Sama ta Turkiyya ta kaddamar a 2017.

Jirgin ya kuma cika muhimman ka’idojin fannin horar da matukan jiragen sama a zamanance ta hanyar kwazo da ya nuna a sararin samaniya.

Zai maye gurbin tsofaffin jiragen bayar da horo da ake da su a yanzu.

Jirgin yaki na Hurjet na da tsayin mita 13.4, fika-fikansa kuma na da fadin mita 9.5.

Turkiyya ta zama kasar da ke fitar da kayan tsaro zuwa kasashen ketare inda sojojin kasa da dama suke amfani da kayayakinta, in ji Shugaba Erdogan.

TRT World