Erdogan ya ce "Ina Allah wadai da wannan ɗanyen aikin da aka kai kan cibiyoyin masana'antun ƙera jiragen sama na Turkiyya." / Hoto: AA

Shugabanni daga ƙasashen duniya sun yi tur da Allah wadai da harin ta'addanci da aka kai masana'antar ƙera kayayyakin jiragen sama a babban birnin Turkiyya, inda mutum biyar suka yi shahada sannan wasu 22 suka jikkata.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi Allah wadai da harin na hedkwatar Masana'antar Ƙera Jiragen Sama ta TAI a birnin Ankara a ranar Laraba.

Erdogan ya ce "Ina Allah wadai da wannan ɗanyen aikin da aka kai kan cibiyoyin masana'antun ƙera jiragen sama na Turkiyya."

Rasha

Shugaban Rasha Vladimir Putin shi ma ya yi Allah wadai da harin a yayin taron kungiyar BRICS da Erdogan ya halarta a matsayin baƙo a can ƙasar.

"Ya mai girma Shugaban Ƙasa da abokan aiki, muna matukar farin cikin maraba da kai zuwa Kazan, amma kafin mu fara aiki, ina so in jajanta maka dangane da harin ta'addancin da ya faru. Rahotannin da ke fitowa daga kafafen yaɗa labarai sun nuna cewa an kai harin ta'addanci a Turkiyya. " in ji Putin.

Amurka

Ita ma Amurka ta yi Allah wadai da harin ta'addancin, inda Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya ce, "Amurka tana tare da ƙawarmu Turkiyya, kuma tana matuƙar yin Allah wadai da harin ta'addancin da ya faru a yau. Muna jajantawa wadanda abin ya shafa da iyalansu," in ji Blinken a saƙon da ya wallafa a shafin X.

Shi ma mai magana da yawun Majalisar Tsaro ta Fadar White House John Kirby ya yi Allah wadai da harin.

“A safiyar yau, addu’o’inmu na tare da dukkan wadanda abin ya shafa da iyalansu, da ma al’ummar Turkiyya a wannan mawuyacin lokaci,” in ji shi.

NATO

Shi ma Sakataren Ƙungiyar Tsaro ta NATO Mark Rutte ya yi Allah wadai da harin.

"Muna yin Allah wadai da ta'addanci a kowane salo kuma muna sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa," in ji Rutte.

"NATO tana tare da ƙawarta Turkiyya," ya ƙara da cewa.

Tarayya Turai

Babban jami'in kula da Harkokin Waje na Tarayyar Turai Josep Borrell ya yi Allah wadai da harin ta'addanci ta kowane ɓangare, a cikin wani saƙon da ya wallafa a shafin X bayan kai harin.

Ya ce " EU na nuna goyon baya ga Turkiyya a wannan mawuyacin lokaci."

Azerbaijan

Ita ma Azabaijan ta yi Allah-wadai da harin, inda ta ƙara da cewa Baku tana tare da "'yar'uwarta Turkiyya."

Faransa

Shugaban Faransa Emmanuel Macron shi ma ya yi Allah wadai da "harin ta'addancin da aka kai Ankara cikin kakkausar murya," a wani sakon da ya wallafa a shafin X.

Ya ƙara da cewa, al'ummar Faransa sun ji takaici tare da tausaya wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu a harin sun kuma jajanta musu.

Jamus

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya bayyana a shafin X cewa: "Na yi matuƙar kaɗuwa da rahotannin mutanen da suka mutu da kuma wadanda suka jikkata a Ankara, muna yin Allah wadai da ta'addanci ta kowace siga kuma muna goyon bayan abokiyar hulɗarmu Turkiyya."

The Netherlands

Shi ma firaministan kasar Holland Dick Schoof ya miƙa sakon ta'aziyyarsa ga Shugaba Erdogan, yana mai cewa kasar Netherlands ta yi Allah wadai da duk wani nau'in ta'addanci. Muna tausaya wa Turkiyya kuma muna sa ido sosai kan lamarin.

Austria

Shugaban kasar Austriya Karl Nehammer shi ma ya yi Allah-wadai da harin, yana mai cewa: "Ta'addanci da tashin hankali ba su da gurbi a cikin al'ummarmu."

Kosovo

Ita ma Kosovo ta yi Allah wadai da harin, inda ta bayyana goyon bayanta ga Turkiyya.

"Muna tare da ƙawayarmu, Turkiyya, biyo bayan harin ta'addancin da aka kai yau a Ankara, muna miƙa ta'aziyyarmu ga iyalai da 'yan'uwan ​​wadanda abin ya shafa. Ta'addanci da tashin hankali ba su da gurbi a duniyarmu!" in ji Shugaba Vjosa Osmani a saƙonsa a shafin X.

Slovenia

Slovenia ma ta bi sahun yin Allah wadai da ''mummunan'' harin, inda mataimakin firaministan kasar Tanja Fajon ya ja hankali kan adadin fararen hula da suka mutu.

"Na yi Allah wadai da mummunan harin da aka kai - wanda ya yi sanadin rayukan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba - a Turkiyya a yau. Ta'addanci da kowane irin tashin hankali ba su da waje - a cikin al'ummomin dimokuradiyya. Muna ta'azaiyar wadanda aka kashe da kuma jajanta wa 'yan'uwansu," in ji shi.

Ireland

Ma'aikatar Harkokin Wajen Ireland ta fada a shafin X cewa "Ireland ta yi tir da mummunan harin da aka kai a Turkiyya a yau."

Serbia

Shugaban Sabiya Aleksandar Vucic ya bayyana "damuwa" game da harin ta'addanci da aka kai a Ankara.

"Serbiya ta yi Allah wadai da duk wani nau'in ta'addanci, kuma tana goyon bayan Turkiyya da al'ummarta," in ji shi, yana mai miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda abin ya shafa, "kuma ina yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa."

Canada

Ofishin Jakadancin Canada a Turkiyya ya fitar da irin wannan bayani da kakkausar murya, inda ya kara da cewa Ottawa na goyon bayan Turkiyya, "abokiyarmu kuma aminiyarmu, a wannan mawuyacin lokaci."

TRT World