Da yake magana a wajen wani taron manema labarai a Ankara, Shugaban Turkiyya Erdogan ya godewa shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud da Firaminitsan Ethiopia Abiy Ahmed saboda “sasantawa mai tarihi” da suka yi. / Hoto:AA

Ƙungiyar Haɗin kan Ƙasashen Gabashin Afirka ta yi jinjina dangane da wata yarjejeniya da aka cimmawa tsakanin Somalia da Habasha wadda ta kawo ƙarshen zaman ɗarɗar wanda aka shafe kusan shekara guda ana yi bayan cim ma yarjejeniyar a Ankara babban birnin Turkiyya.

Workneh Gebeyehu, babban sakataren ƙungiyar IGAD, ya bayyana godiyarsa ga shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan bisa ƙoƙarinsa wajen karɓar baƙuncin taron da kuma gudanar da tattaunawar da ta samar da mafita a Ankara da yammacin Laraba.

Da yake amincewa da sadaukarwar Erdogan ga diflomasiyya da haɗin gwiwar yanki a matsayin wani muhimmin al'amari na cim ma yarjejeniyar, Gebeyehu ya jaddada muhimmancin "irin wannan yunƙurin diflomasiyya wajen tunkarar ƙalubalen da ake fuskanta tare da samar da kwanciyar hankali da wadata a yankin kusurwar Afirka."

Son haɗin kai

Ƙasashen na Gabashin Afirka na ta zaman doya da manja a tsakaninsu tun bayan da Habasha ta cim ma yarjejeniya da yankin Somaliland da ya ɓalle a ranar 1 ga Janairu domin amfani da tashar ruwanta ta Berbera. Turkiyya na ta ƙoƙari domin kawo ƙarshen rashin jituwar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan da Firaministan Habasha Abiy Ahmed da Shugaban Somalia Hassan Sheikj Mohamud sun gudanar da taron manema labarai a Ankara babban birnin Turkiyya inda suka sanar da cim ma yarjejeniya a tsakaninsu a lokacin da Turkiyya ta jagoranci sasancin.

A cikin sanarwar hadin gwiwa, kasashen Afirka biyu sun tabbatar da 'yancin kan juna, da haɗin kan juna, inda suka kuduri aniyar kaddamar da tattaunawa da taimakon Turkiyya a karshen watan Fabrairun 2025 tare da kammala ta cikin watanni hudu.

A shekara ta 1991, Eritrea ta samu 'yancin kai daga Habasha, wanda ya kai ga kafa kasashe biyu. Rabuwar ta sa Habasha ta rasa hanyar shiga tekun bahar maliya kai tsaye da kuma manyan tashoshin jiragen ruwa.

AA