Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa, Turkiyya za ta dauki matakin tabbatar da cewa shugabannin siyasa da na soja da suka yi kisan gilla a Gaza sun fuskanci shari'a a kotunan duniya.
Da yake kiran Isra'ila a matsayin "kasa ta 'yan ta'adda" a ranar Laraba, shugaban na Turkiyya ya zargi Tel Aviv da aiwatar da dabarun lalata dukkanin Gaza tare da mazaunansa.
Da yake jawabi a wani taron kungiyar 'yan majalisu na Jam'iyyar (AK) a Ankara, Erdogan ya aika sako ga firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, yana mai cewa: "Kuna yin barazana da bam na nukiliya, bam din nukiliya. Abin da kuke da shi din ba komai ba ne, kai mai gushewa ne."
Ya kara da cewa, idan Isra'ila ta ci gaba da kashe-kashen da take yi, za a rika kallonta a ko ina a duniya a matsayin wata kasa ta 'yan ta'adda da ake Allah wadai da ita.
"Ba za mu yi shakkar cewa Hamas (ta ƙunshi) mayaka masu fafutukar kare ƙasarsu ne, duk da rashin jin daɗin da hakan zai sa wasu su ji.
Erdogan ya ƙara da cewa zai kuma yi wa shugabannin ƙasashen da suka ƙi kaɗa ƙuri'ar neman a tsagaita wuta a Gaza a taron Majalisar DInkin Duniya.
Hare-hare ba ƙaƙƙautawa
Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare ta sama da ta ƙasa a Gaza tun bayan harin da ƙungiyar Falasɗinawa ƴan gwagwarmaya ta Hamas ta kai sansanonin sojin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba.
Aƙalla Falasɗinawa 11,320 aka kashe, ciki har da mata da yara kusan 7,800, sannan mutum 29,200 suka jikkata, a cewar alkaluman hukumomin Falasɗinu.
Dubban gine-gine da suka haɗa da asibitoci da masallatai da coci ne suka rushe ko suka lalace a hare-haren Isra'ila.
Adadin wadanda suka mutu a Isra'ila, ya kai 1,200, a cewar alkaluman hukuma.