Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya ce Turkiyya za ta haɗa kai da Afirka ta Kudu a ƙarar da ƙasar ta kai gaban Kotun Duniya dangane da kisan kiyashin Isra'ila.
"Turkiyya za ta buƙaci ta haɗa kai da Afirka ta Kudu kan shari'ar kisan kiyashin Isra'ila," kamar yadda Fidan ya bayyana a ranar Laraba.
A yayin da yake jawabi a wani taron manema labarai bayan tattaunawa da Ministan Harkokin Wajen Indonesia Retno Marsudi a ma'aikatar, Fidan ya yi magana kan lamarin inda ya bayyana abubuwan da aka tattauna a yayin ziyararsu a Riyadh, babban birnin Saudiyya.
Fidan ya bayyana cewa a lokacin tattaunawarsa ta diflomasiyya da ƙasashen da suka amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa, daga ciki har da Ƙungiyar Haɗin-kan Ƙasashen Musulmi ta OIC da ta Tarayyar Ƙasashen Larabawa, wasu daga cikin ƙasashen sun nuna shirinsu na ɗaukar matsaya dangane da batun.
Ci gaba da shirye-shiryen shari'a
Fidan ya bayyana ƙasashen Nicaragua da Colombia a matsayin ƙasashen da tuni suka ɗauki matsaya kan wannan shari'ar, inda ya jaddada niyyar da Turkiyya ke da ita na shiga wannan shari'ar.
"Dangane da tantancewar da muka yi a yau, mun gabatar da sakamakon ga mai girma shugaban kasarmu, kuma bisa ga shawarar da aka yanke ta siyasa, a karon farko ina sanar da cewa Turkiyya ta yanke shawarar shiga shari'ar da Afirka ta Kudu ke yi da Isra'ila a Kotun Duniya," in ji Fidan.
A yayin da yake sa ran samun ci gaba a shari'ar da ake yi a gaban Kotun Duniya, Fidan ya jaddada irin ƙoƙarin da Turkiyya ta jima tana yi domin shirya wa wannan matakin.
Fidan ya ƙara da cewa Ankara za ta ci gaba da goyon bayan Falasɗinawa "ta kowane hali."