Abin takaici ne ganin yadda rahoton na Amurka ya kawar da kai kan babban kokarin da Turkiyya take yi na hana safarar mutane, in ji Ankara. / Hoto: AP Archive

Turkiyya ta caccaki wani rahoto na Amurka da ya yi zargin cewa Ankara na yin amfani da kananan yara a matsayin sojojin sa-kai, inda ta bukaci Washington ta tuna yadda take goyon bayan kungiyoyin ta'addanci da ke daukar kananan yara aikin ta'addanci a Syria.

"Mun yi watsi da daukacin zarge-zargen da aka alakanta da kasarmu cewa muna daukar kananan yara a matsayin sojojin sa-kai bayan mun sanya hannu kan takardar da ke kyamar tursasa wa yara shiga irin wannan aiki kamar yadda MDD ta tsara kuma muna aiwatar da abubuwan da ke cikin takardar," in ji sanarwar da Ma'aikatar Wajen Turkiyya ta fitar ranar Asabar din nan.

"Abin takaici ne ganin yadda aka kawar da ido kan babban kokarin da Turkiyya take yi na hana safarar mutane inda aka saka ta a jerin kasashen da ke daukar kananan yara a matsayin sojojin sa-kai a karkashin rahoton 'Hana Daukar Yara a Sojin Sa-kai na Ma'aikatar Tsaron Amurka na 2023," a cewar sanarwar.

Turkiyya ta ce tana yin kokari na hana aikata laifukan da suka shafi safarar mutane da hukunta wadanda aka samu da laifi da kare wadanda suka fada cikin wannan yanayi a yayin da kuma take karfafa hadin kai da take bai wa kasashen duniya na kawar da wannan matsala.

Ta kara da cewa an sake siyasantar da batun 'yancin dan'adam.

Türkiyya ta ce Amurka ce take bayar da tallafin kudi da kayan aiki ga kungiyoyin ta'addanci irin su PKK/YPG, wadanda ke tursasa wa kananan yara shiga aikin ta'ddanci a Syria da Irakiq, sannan ta nemi Washington da ta kalli kashin da ke jikinta.

"Wannan batu ya sanya babbar alamar tambaya game da sahihancin bayanan da ake samu daga hukumomin Amurka. Wannan cin-fuska ne, wanda ba zai yi wa kawancenmu dadi ba, kuma dole mu taka muku birki," a cewar sanarwar.

Daukar yara da kungiyar da Amurka ke goya wa baya ke yi

Turkiyya ta bayyana cewa akwai laifuka da dama da kungiyar “Syrian Democratic Forces” ko kuma SDF a karkashin ikon kungiyar ta’ddanci ta PKK/YPG ke aikatawa, kamar daukar yara karfi da yaji da garkuwa da su da kuma hana su ‘yanci da amfani da makarantu a Syria.

Turkiyyar ta bayyana cewa hakan na kunshe a cikin wani rahoto na bincike da wata hukuma ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi kan Syria a ranar 12 ga watan Satumba.

“Bugu da kari wani misali na baya-bayan nan game da munanan abubuwan da kungiyar ta yi shi ne a Deir ez-Zor,” in ji sanarwar da ma’aikatar wajen ta fitar.

Da take karin haske kan cewa rahoton da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar kan kasar Iraki a shekarar 2022 ya fito karara cewa 'yan ta'addar PKK na tilasta wa daruruwan yara 'yan kabilar Yezidi aiki tare da su da yin garkuwa da su domin cusa musu akidarsu, kamar yadda Turkiyya ta bayyana cewa:

"Muna tunatar da cewa binciken ayyukan zalunci da manyan laifuka na kungiyar ta'addanci ta 'yan aware na daga cikin muhimman abubuwan ya rataya a wuyan Amurka.

“A matsayin kasar da ta kuduri aniyar aiwatar da yarjejeniyoyin yanki da na kasa da kasa, Turkiyya za ta ci gaba da dagewa da nufin dakile aikata laifukan safarar mutane,” in ji ta.

TRT World