Turkiyya za ta ci gaba da bayar da gudunmowa ga matakan da za su tabbatar da wanzuwar zaman lafiya mai dorewa, janyewar Isra'ila daga Gaza, musayar fursunoni, in ji ma'aikatar./ Hoto: AA Archive

Turkiyya ta yi maraba da matakin da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya dauka na kira da a tsagaita wuta a yankin Gaza na Falasdinu, in ji Ma'aikatar Harkokin Waje inda ta bayyana hakan a matsayin "Mataki mai muhimmanci".

Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar a ranar Talata ta ce, "Muna goyon bayan matakin da Kwamitin Tsaro na MDD ya dauka mai lamba 2735 a ranar 10 ga Yuni, wanda ke da manufar samar da tsagaita wuta a Gaza, kuma muna yi masa kallon muhimmin matakin kawo karshen kisan kisan kiyashin da ake yi."

"Muna kuma maraba da na'am da nuna goyon baya ga matakin da Hamas ta yi don tsagaita wuta," in ji sanarwar.

Sanarwar na zuwa ne bayan da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince da wani kudirin daukar mataki da Amurka ta gabatar da ke goyon bayan shawarar da Shugaban Kasar Amurka Joe Biden ya bayar na tsagaita wuta a Gaza, Rasha ta ƙi jefa ƙuri'a, inda sauran mambobi 14 suka nuna goyon baya ga matakin.

"Ya zama dole Isra'ila ta sanar da ita ma tana goyon bayan tabbatar da tsagaita wuta da kuma aiki da dukkan sharuddan da matakin ya tanada," in ji Ma'aikatar.

Ma'aikatar ta ƙara da cewa Turkiyya za ta ci gaba da bayar da gudunmawa ga matakan da za su tabbatar da wanzuwar zaman lafiya mai ɗorewa da janyewar Isra'ila daga Gaza da musayar fursunoni da mayar da Falasdinawa gidajensu da ke Gaza da bayar da dama ga kai kayan agaji ga jama'a da kuma sake gina yankunan da aka rushe.

TRT World