Ministan Harkokin Waje Hakan Fidan ya yi kira ga ƙasashen duniya da su ƙalubalanci ƙarfin ikon Amurka kan neman zama mamba a Majalisar Ɗinkin Duniya da Falasɗinu ke yi, su kuma amince da Falasɗinu ɗin a matsayin 'yantacciyar ƙasa.
"Rashin adalci ne a hana Falasɗinu zama mambar Majalisar Dinkin Duniya. Muna kira ga ƙasashen duniya da su ƙalubalanci wannan rashin adalcin, su kuma amince da 'yantacciyar aƙsar Falasɗiun," in ji Fidan a ranar Lahadi yayin taron manema labarai da ya gabatar tare da takwaransa na Murtaniya Mohamed Salem Ould Merzouq a birnin Istanbul.
A yayin ganawar da Merzouq, Fidan ya ce sun tattauna kan "kisan kiyashin da ake ci gaba da yi a Gaza," kuma kamar Turkiyya, Mustaniya ma na aiki da kyakkyawar manufa game da batun Falasdin, musamman halin da ake ciki a Gaza, kuma na bayar da dukkan goyon baya.
Gaza, yana mai kara wa da cewar "Za mu ci gaba da hada kai don ganin an tsagaita wuta nana da nan, da kuma tabbatar da kai kayan agaji ba tare da wata matsala ba."
Ya kuma ce kokarin kasashen biyu zai ci gaba ba tare da wata matsala ba har zuwa lokacin da za a tabbatar da kafuwar 'yantacciyar kasar Falasdinu, mai babban birnin a Gabashin Jerusalem duba da yarjeeniyar da ta fitar da iyakokin 1967.
Da yake tabo batun alakar Turkiyya da Murtaniya, Fidan ya kara da cewa Murtaniya ta zama kasa mai zaman lafiya a yankin, kuma Turkiyya za ta ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen inganta kawancen tsaro da hadin kan cigaban tattalin arziki domin zaman lafiya da habakar yankin.
Ya ce "Muna da niyyar kafa hukumar hadin kan tattalin arziki a karon farkotsakanon Tukiyya da Murtaniya da zarar an cimma matsaya da kammala shirye-shiryen yin hakan.
Fidan further said they had the opportunity to thoroughly evaluate the bilateral relations during the meeting, adding that they reaffirmed their determination to enhance cooperation in all fields, particularly in economic and commercial matters.
Fidan ya kuma bayyana irin gudunmowar da jiragen saman Turrkish Airlines na Tukiyya zuwa Murtaniya, wanda wnai bangare ne na tattaklin arziki tsakanain kasashen biyu.
Ya kara da cewar suna matukar murna da ganin daliban Murtaniya na karatu a Turkiyya a karkashin tallafin karatu na gwamnatin Turkiyya.
Fidan ya kuma bayyana muhimmancin Ankara wajen tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da yalwa a kasar ta yankin Sahel da ke Yammacin Afirka.
Ya kuma bayyana matukar muhimmancin samar da tsaro a yankin.
A nasa bangaren, Ministan Harkokin Wajen Murtaniya Merzouq ya bayyana cewa albarkatun kasa, iskar gas, makamashi mai sabuntuwa da tsaftataccen makamashi da ke Turkiyya na da muhimmanci ga Murtaniya.
Merzoud ya kuma ce tare da Fidan sun tattauna kan batutuwa da dama da shafi alakar kasahensu, tsaro, zaman lafiya, sufuri, kula d alafiya, ilimi, noma da kiwo.
Ministan ya kuma bayyana irin kyakkyawar alaka da fahimtar juna da ke tsakanin Shugaban Kasar Murtaniya Mohamed Ould Ghazouani da Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.
Merzouq ya karkare da tabo batu Nuna Kyama ga Musulunci, inda ya gode wa Turkiyya bis akokarin da take yi a wannan bangare.