Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya shaida wa takwaransa na Amurka cewa bai kamata a bar ƙungiyoyin ta’addanci irin su PKK da Daesh su amfana da abin da ke faruwa a Syria ba.
Jami’ia na diflomasiyya biyu sun tattauna ta waya ranar Juma’a don tunkarar yanayin da ake ciki a Syria, kamar yadda majiyoyin diflomasiyyar Turkiyya suka bayyana.
Da yake jaddada muhimmancin kaucewa maimaita kuskuren da aka yi a baya, Fidan ya nuna cewa a yanayin da ake ciki, ya kamata gwamnatin Syria ta ɗauki babban matakin tattaunawa da ‘yan hamayya, ta kuma fara lalubo hanyoyin warware matsalar a siyasance.
Ya bayyana cewa ya wajaba duka masu ruwa da tsaki a yankin su taka rawar da ta kamata.
Fidan ya kuma ce yana da muhimmanci a ɗauki dukkan matakan da suka dace wajen ganin an hana makamai masu guba da gwamnatin Syria ke da su daga zama wata barazana a yankin.
Da yake jaddada muhimmancin kai kayayyakin agaji Syria, Fidan ya ce Turkiyya ta samar da tallafin da ya kamata.
Yadda yaƙin Syria ke sauya salo
Dakarun hamayya a Syria sun ƙwace wurare masu yawa a arewa maso yammaci da kudancin ƙasar, abin da ya bude wata sabuwar matsala a Gabas ta Tsakiya da ke fama da raɗaɗin kisan ƙare dangin da Isra’ila ke yi a Gaza da wasu wuraren.
Arangama ta ɓarke a ranar 27 ga Nuwamba tsakanin dakarun gwamnatin Syria da ƙungioyin hamayya a birnin Aleppo (Halab) dake yammacin ƙasar. Yaƙin ya haifar da wani irin sauyi a yadda ake riƙe da iko a ƙasar.
Zuwa 30 ga watan Nuwamba, dakarun hamayya sun ƙwace iko da tsakiyar birnin Aleppo, sun karɓe iko da gaba ɗaya yankin Idlib. Nasarar da suka samu ta sauya gaba ɗaya yadda yaƙin ke tafiya.
Ana ganin ƙwace Aleppo da ‘yan hamayya suka yi a matsayin wata nasara, domin birnin mai tarihi — wanda kuma shi ne birnin mafi yawan jama’a a Syria — ya fuskanaci yaƙi mafi daeɗwa domin neman samun iko da birnin a matakan farko-farko na yaƙin basasar Syria, wanda yayi sanadiyyar kashe mutane fiye da 500,000 ya kuma raba fiye da miliyan 10 daga gidajensu tun daga 2011.
A ranar 1 ga Disamba Dakarun Syria sun ƙaddamar da wani yunƙuri da aka yi wa take Operation Dawn Freedom a Tel Rifaat, inda suka durfafi ƙungiyar ta’addanci ta PKK/YPG. Yunƙurin ya yi nasar ‘yantar da ‘yankin, aka kori ‘yan ta’adda daga yankin.
Zuwa ranar 5 ga Disamba dakarun hamayya sun ƙwace Hama sannan suka fara nausa wa Homs, abin da ya sa yakin neman iko da Syria ya ƙara ƙamari.
A ranar 6 ga Disamba, cibiyar birnin yankin Daraa dake kan iyakar Syria da Jordan ya faƙa ƙarƙashin ikon ƙungiyoyin hamayya.