Turkiyya ta yi kakkausar suka kan harin da Isra'ila ta kai kan tantunan fararen hula a Khan Younis, yankin da aka kebe a Zirin Gaza.
Harin ya yi sanadin mutuwar Falasdinawa da dama, kuma jami'an Turkiyya sun bayyana shi a matsayin wani mummunan tashin hankali.
A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar a jiya Talata, Turkiyya ta yi Allah wadai da harin a matsayin kisan kiyashi, inda ta zargi gwamnatin Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu da aikata wani abu da ta kira "sabon laifi" na cin zarafin bil'adama.
Ma'aikatar Harkokin Wajen kasar ta ce "Gwamnatin Netanyahu mai kisan kiyashi ta kara wani sabon laifi a cikin jerin laifukan yaki."
"Wadanda suka aikata wadannan laifuka za a gurfanar da su a gaban dokokin kasa da kasa."
Gwamnatin Turkiyya ta kira lamarin a matsayin ci gaba da irin yadda gwamnatin Isra'ila take aikata laifukan yaki tare da jaddada cewa dole ne a hukunta wadanda suka aikata irin wannan aika aika a karkashin dokokin kasa da kasa.
La'anar da Turkiyya ta yi na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula da kuma damuwar da kasashen duniya ke nunawa dangane da matsalar jin kai a Gaza.
Yayin da al'amura ke ci gaba da tabarbarewa a Gaza, Turkiyya ta sha alwashin ci gaba da goyon bayan Falasdinawa, inda ta bukaci kasashen duniya da su dauki kwakkwaran mataki kan masu aikata irin wadannan laifuka.
Yakin kisan kare dangi da Isra'ila ke yi a Gaza, wanda yanzu ya cika kwanaki 340, ya kashe Falasdinawa 40,988 - akasari mata da kananan yara.