Turkiyya ta yi Allah wadai da wani hari da Isra'ila ta kai wa Iran a cikin dare da "kakkausar murya."
"Isra'ila wadda ke aikata kisan kiyashi a Gaza, da kuma shirin mamaye Gaɓar Yamma da Kogin Jordan tare da kashe fararen hula a kullum a Lebanon, wannan harin ya sa yankinmu na dab da faɗawa cikin babban yaƙi," kamar yadda Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta sanar a ranar Asabar.
"A yanzu dai ta bayyana cewa kawo karshen ta'addancin Isra'ila a yankin ya zama wani aiki mai cike da tarihi na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a duniya.
Don haka Ankara ta yi kira ga kasashen duniya da su dauki matakin gaggawa don tabbatar da doka da dakatar da gwamnatin Isra'ila, in ji ta.
"Turkiyya ta sake nanata cewa ba ma son wani yaki, tashin hankali, ko rashin bin doka da oda a yankinmu," in ji ta.
Don samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, ya zama wajibi kasashen yankin da wadanda ba na yankin ba su yi aiki da hankalisu, in ji shi.
Akalla sojojin Iran biyu ne suka rasu a ranar Asabar a lokacin da sojojin Isra'ila suka kai wa Iran hari a wani martani ga harin makami mai linzami da Tehran ta kai kan Isra'ila a ranar 1 ga watan Oktoba.
Fadar White House ta ce dole ne hare-haren na Isra'ila ya kawo karshen musayar wuta kai tsaye tsakanin bangarorin biyu, tana mai gargadin Tehran da "yaba wa aya zaƙinta" idan ta mayar da martani.