Turkiyya ta shiga fafutukar ƙasashen duniya don ganin an hukunta Isra'ila kan aikata laifukan yaƙi

Turkiyya ta shiga fafutukar ƙasashen duniya don ganin an hukunta Isra'ila kan aikata laifukan yaƙi

A hukumance Ankara ta shiga ƙarar kisan kiyashin da aka kai Isra'ila a Kotun Ƙasa da Ƙasa Mai Hukunta Manyan Laifuka.
Ana zargin Isra'ila da aikata laifukan yaki da kisan kiyashi a kan Falasdinawan Gaza. / Hoto: AA Archive

Yunƙurin Turkiyya na bin sahun Afirka ta Kudu na ƙalubalantar kisan kiyashin Isra'ila ya ƙara ƙarfi da yawan lauyoyi a Kotun Ƙasa da Ƙasa Mai Hukunta Manyan Laifuka don gurfanar da Tel Aviv a gaban kotun saboda aikata laifukan yaƙi kan Falasɗinawan Gaza, in ji jami'an diflomasiyyar Turkiyya yayin tattaunawa da TRT World.

Bayan Afirka ta Kudu ta tunkari ICJ a shekarar da ta gabata, tana bayyana wa kotun cewar yaƙin Isra'ila ya janyo rikicin jinƙai kuma ya saɓa wa taron Hana Kisan Kiyashi na 1948, ƙasashe da dama sun bi sahunta.

Za a ɗauki shekaru 4 zuwa 5 kafin ICC ta fitar da hukuncin ƙarshe, amma ana bayyana cewar idan aka samu masu shigar da ƙara da yawa, to za a hana afkuwar irin wannan abu a nan gaba.

"Bayyana aniyar Turkiyya ya fi kowanne gamsassun bayanai, masu fahimta cikin sauƙi, kuma masu ɗauke da hujjoji da yawa. Wannan abu na bai wa ICJ ƙarfin gwiwar fassara tanade-tanaden Taron Haramta Kisan Kiyashi daidai," in ji jami'in na Turkiyya.

"Bayanan da Ankara ta fitar ya hado da Sashe na 1, 2 da 3 na Taron da kuma ƙarfafa buƙatar ɗaukar matakan bincike da gurnawarwa a gaban kotu saboda aikata kisan kiyashi."

Duk wata ƙara a ICJ na iya zama rikitacciya a ɓangaren lauyoyi da alkalai da za su yi ta muhawara, wanda hakan ka iya sanya shari'ar ta dauki tsawon shekaru hudu.

A watan da ya gabata, ICJ ta fitar da sanarwar bayar da shawara mai tarihi, tana fada wa Isra'ila cewa mamayar da isra'ila ke yi wa yankunan Falasdinawa Yammacin Gabar Kogin Jordan, Kudus a Gaza ba ya bisa ka'ida.

Turkiyya ta kuma ce bayanan da ta gabatarwa kotun za su goyi bayan ra'ayin ICJ game da mamayar yankunan Falasdinawa da yankunan da ba sa kan ka'ida.

"Wannan kawance zai karfafi muhawarar Turkiyya da habaka muhimmancin kai karar."

Jami'an Turkiyya sun ce bayanin muhawarar Turkiyya a gaban kotun da nazari mai saukin fahimta "na iya zama wani misali mai daraja ga wani abu irin haka a nan gaba wanda zai kawo ci gaba a dokokin jinkai na kasa da kasa".

"Shiga ƙarar da Ankara ta yi ba iya rikicin Gaza na yanzu zai warware ba, zai kuma ƙarfafa tsarin shari'a na duniya wajen magance irin hakan a nan gaba."

'Laifukan yaƙin da Isra'ila ke aikata wa karara'

Majiyoyin diflomasiyya sun ce "laifukan yaƙi, cin zarafin ɗan'adam da kisan kiyashi" da Isra'ila ke yi na samun goyon baya daga yadda duniya ta zuba wa Isra'ila idanu tana yin yadda take so ba tare da ƙalubalantar ta ba.

"Domin kawar da wannan fahimta, dole ne kasashen duniya su dauki mataki cikin gaggawa don tabbatar da cewa kotuna irin su ICJ da ICC sun dauki matakin shari'a kuma a tabbatar da an aiwatar da matakin."

A matsayin kasar da ta sanya hannu a Taron Haramta Kisan Kiyashi na 1948, Turkiyya na da alhakin dokokin kasa da kasa da suka haramta kisan kiyashi ko hukunta masu kisan kiyashin.

"Shigar Turkiyya shari'ar na bayyana ƙudurinta na aiki da waɗannan dokoki kuma ta zama abar koyi ga sauran ƙasashe a lokacinda ake kokarin magance wani rikici na jinƙai."

A ranar Laraba 7 ga Agustan 2024 aka mika wa ICJ takarun shigar da karar na Turkiyya.

Kasashen Nicaragua, Colombia, Libya, Mexico, Falasiɗnu da Sifaniya sun miƙa takardu kotun don shiga ƙarar batun. Har yanzu kotun ba ta ce komai bai game da miƙa takardun.

TRT World