Turkiyya ta la'anci kisan gilla da aka yi wa shugaban Hamas Ismail Haniye a wani hari ta sama da Isra'ila ta kai Iran.
"Muna la'antar kisan gilla ga Shugaban Siyasar Hamas Ismail Haniyeh a wani mummunan hari a Tehran," in ji sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar a safiyar Laraba.
"Wannan hari na da manufar yaɗa rikicin Gaza a dukkan yankin. Idan ƙasashen duniya ba su ɗauki matakan dakatar da Isra'ila ba, yankinmu zai fuskanci manyan rikice-rikice," in ji sanarwar.
"An sake nuna cewar gwamnatin Netanyahu ba ta da niyyar rungumar zaman lafiya."
Ma'aikatar ta ƙara da cewa "Muna miƙa saƙon ta'aziyya ga jama'ar Falasɗinawa da suka sadaukar da dubban ɗaruruwan shahidai irin su Haniyeh don ganin sun zauna lafiya a ƙasarsu, ƙarƙashin inuwar ƙasa mallakinsu."
Turkiyya ta yi alƙawarin ci gaba da goyon bayan "buƙatun jama'ar Falasɗinu."
Haniyeh, fitaccen ɗan siyasar Falasɗinu da ƙungiyar gwagwarmaya, ya kasance babban jigo kafin da lokacin yaƙin kisan kiyashin Isra'ila a Gaza da aka mamaye.