Turkiyya ta lalata wurare 29 na kungiyar 'yan ta'adda ta PKK a arewacin Iraki da Syria, a cewar Ma'aikatar Tsaro kasar, awanni bayan mayakan PKK sun kashe sojojin Turkiyya tara a harin da suka kai sansaninsu da ke arewacin Iraki.
"An kai hare-hare ta sama a wuraren 'yan ta'adda da ke yankunan Metina, Hakurk, Gara da kuma Qandil a Iraki da arewacin Syria, a matsayin kare kai kamar yadda Sashe na 51 na dokar MDD ya ce," in ji wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar a yau Asabar.
An kai hare-haren ne a yayin da daraktan sadarwa na Turkiyya ya bayar da sanarwa game da wani muhimmin taro kan sha'anin tsaro da Shugaba Recep Tayyip Erdogan zai jagoranta a Istanbul.
"Bisa umarnin shugaban kasarmu Recep Tayyip Erdogan, za a gudanar da taro kan sha'anin tsaro ranar Asabar, 13 ga watan Janairu da misalin karfe biyu da rabi na rana [1130GMT] a Ofishin Dolmabahce da ke Istanbul," in ji Fahrettin Altun a sakon da ya wallafa a shafin X, wanda a baya ake kira Twitter.
Ya ce manyan ministoci da jami'an tsaro cikin har da ministocin harkokin waje da na harkokin cikin gida da na tsaro da hafsoshin tsaro da manyan jami'an hukumomin leken asiri za su halarci taron.
Ministan Harkokin Kasashen Waje Hakan Fidan, da takwaransa na Cikin Gida Ali Yerlikaya, da Ministan Tsaro Yasar Guler, da Hafsan Tsaro Metin Gurak da shugaban Hukumar Leken Asiri ta (MIT) Ibrahim Kalin za su halarci taron, in ji Altun.
Tun da farko, Altun ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan sojojin da aka kashe, yana mai cewa, "Muna yin addu'a tare mika sakon ta'aziyya ga iyalan jajirtattun sojojinmu da suka sadaukar da kawunansu domin kare kasarmu."