Turkiyya ta amshi mutane 292 da suka jikkaka da kuma marasa lafiya daga Gaza don basu kulawa da magani tun daga lokacin da Isra'ila ta fara kai munanan hare-hare a yankin Falasdinawa a shekarar  bara. / Hoto: AA      

Turkiyya ta dauki karin majinyata 85 da kuma wadanda suka jikkata daga yankin Gaza na Falasdinu daga Masar zuwa kasar, a cewar wata sanarwa da Ministan lafiya na kasar Fahrettin Koca ya fitar.

Ranar Alhamis da daddare ne wasu jirage biyu dauke da marasa lafiya da 'yan'uwansu suka sauka a Ankara babban birnin kasar.

An kai jimillar marasa lafiya 85 da kuma wadanda suka jikkata daga Gaza zuwa Turkiyya daga Masar da maraice, a cewar sanarwar da ya wallafa a shafin X.

"Marasa lafiyar sun samu rakiyar tawagar mutum 106, kuma majinyatan za su samu kulawa da kuma magani a kasarmu, "in ji Koca.

Kawo yanzu Turkiyya ta amshi majinyata 292 da suka samu raunuka da kuma marasa lafiya daga Gaza domin ba su kulawa da kuma magani tun daga lokacin da Isra’ila ta soma kai munanan hare-hare a yankin Falasdinawa a shekarar 2023.

TRT World