Turkiyya ta jaddada kudirinta kan  muradunta na ci-gaba. / Hoto: AA

Daraktan Sadarwa na Fadar Shugaban Turkiyya Fahrettin Altun ya soki mujallar The Economist, yana mai zargin buga labaran ƙarya game da shari'o'in da ke gudana a Turkiyya don sukar Shugaba Recep Tayyip Erdogan.

"The Economist har tana da ƙarfin gwiwar ƙalubalantar Shugaba Erdogan, suna so su jirkita gaskiyar abin da ke faruwa kan batutuwan shari’a da bincike wanda bangaren shari’a na Turkiyya mai cin gashin kansa yake jagoranta.

Ita dai wannan mujallar ce da ta yi shiru tsawon watanni a lokacin da Isra’ila ke ci gaba da ta'addancin kisan ƙare-dangi a Gaza, a yanzu tana ƙoƙarin yi mana lacca," in ji Altun a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi.

Ya ci gaba da cewa, "Ba mu da wani abu da za mu koya daga wannan abin da aka wallafa, wanda ya yi watsi da ƙa'idojin shari'a na duniya, wanda kuma yake ba da goyon baya ga Isra'ila ba tare da wani sharaɗi ba, da kuma ƙoƙarin murƙushe masu kare haƙƙin al'ummar Falasɗinu da ake zalunta. Amma akwai abubuwa da yawa da za mu ɗauka a matsayin gargaɗi."

Turkiyya za ta cim ma muradunta

Kazalika Altun ya yi nuni da abin da ya bayyana a matsayin wani yunƙuri da ake kitsawa domin yin kafar-ungulu game da nasarar da Turkiyya take samu a fannin talabjin a duniya. "Wannan yunƙuri, wanda kai-tsaye ta mayar da hankali kan shirin talabijin mai dogon zango na Turkiyya, wani ɓangare ne na babban makirci da ake ƙullawa a fannin siyasa domin cin mutuncin Turkiyya."

Ya jaddada matsayin Turkiyya na cim ma muradunta, yana mai cewa: "Sai dai, a ƙarƙashin jagorancin Shugabanmu, za mu ci gaba da aiki tuƙuru domin ƙarfafa Turkiyya kuma ba za mu bari a kawar da hankalinmu ba ta hanyar yin abubuwan da ba su dace ba."

Altun ya kammala jawabinsa ta hanyar jawo hankali game da amfani da kuɗaɗen al'umma ba yadda ya kamata ba. "A ƙarshe, mun lura cewa ana amfani da wasu kuɗaɗen mutanen birane na ƙasarmu wajen neman suna. Mun bar wannan batu ga ƙasarmu," in ji shi.

TRT World