Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana cewa, Turkiyya na ƙara zage damtse wajen matsin lamba kan Isra'ila ta yadda za ta bi matakin da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya dauka na tsagaita bude wuta a Zirin Gaza na Falasdinu a cikin watan Ramadan.
Recep Tayyip Erdogan ya ce, "Muna matuƙar ƙoƙari na ƙara matsin lamba kan Isra'ila, bayan matakin tsagaita wuta da Kwamitin Sulhu na MDD ya dauka cikin gaggawa," in ji Recep Tayyip Erdogan yayin wani gangamin zabe a gundumar Sancaktepe da ke Istanbul a ranar Juma'a.
A ranar Lahadi ne za a gudanar da zabe a kasar Turkiyya domin zaben shugabannin kananan hukumomi da sauran wakilan kananan hukumomi.
Ya kara da cewa, "Ba za mu tsaya ba har sai Falasdinawa sun ƙwato 'yancinsu da kuma filayensu da aka mamaye, tare da maido da 'yantacciyar kasarsu tare da Gabashin Kudus a matsayin babban birninta."
Ya ƙara da cewa, a ranar Alhamis din da ta gabata ne Turkiyya ta aike da jirgin ruwa na takwas zuwa kasar Masar dauke da kwantenoni 125,000 na abinci ga al'ummar Gaza.
"Muna yin duk abin da za mu iya, da karfinmu, da kuma dukkan albarkatun da muke da su, ba tare da barin komai ba. Kuma za mu ci gaba da yin haka," in ji Erdogan.
"Falasdinawa masu jaruntaka"
Shugaban ya ce yayin da Turkiyya ta yi nasarar shawo kan ƙalubale a Siriya, Somaliya da Karabakh, tana kuma kokarin tinkarar "gwada halin da Gaza da ke ciki."
“Wadanda suke kiran Falasdinawa masu jajircewa da ke kare ƙasarsu a matsayin ‘yan ta’adda, da kuma masu bin son zuciyar masu sha’awar Isra’ila, ba za su iya furta ko kalma daya a kanmu ba.
Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 32,000 a Gaza tun bayan kutsen da Hamas ta yi a kan iyakokin kasar a watan Oktoban da ya gabata, wanda ya yi sanadin mutuwar mutum 1,200.
Hare-haren bama-bamai da mamaya ta ƙasa ya haifar da tarwatsewar jama'a da ɓarna da kuma yanayin yunwa a yankin da aka yi wa ƙawanya.
Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Litinin ya zartas da wani ƙudiri na neman tsagaita wuta cikin gaggawa na watan Ramadan. An kaɗa ƙuri'a 14 ta goyon baya yayin da Amurka kuma ta ƙauracewa hakan.