Za a gudanar da babban taron kafar watsa labaran TRT na TRT World Forum a ranakun 29-30 ga watan Nuwamba, wanda zai haɗo masu jawabi fiye da 150 daga sama da ƙasashe 30 da za su tattauna kan batutuwna duniya.
Za a gudanar da taron, wanda kafar Rediyo da Talabijin ta Turkiyya TRT shirya a ɗakin taro na Istanbul Conference Centre, sannan an yi masa taken “Duniya A Matakin Tsaka-Mai-Wuya: Tunkarar Rikice-Rikice da Sauye-Sauye”.
Taron, wanda aka san shi a matsayin ɗaya daga manyan tarukan kafofin watsa labarai a duniya, a baya ya karɓi baƙuncin dubban baƙi da masu jawabai fiye da 767.
Ana sa ran taron na bana zai ƙunshi muhimman tattaunawa a kan manyan batutuwa na duniya, da suka haɗa da Gabas ta Tsakiya da Gaza, da Turkiyya, da Afirka, da rikicin Rasha- Ukraine, da siyasar yankuna, da yaƙi da tsaro, da yanayi da makamshi, da fasaha, da kafofin watsa labarai, da dokokin duniya da kuma tattalin arziki.
Ana sa ran Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan wanda yake halartar taron a kai-a kai tun 2017, zai gabatar da jawabi kan batutuwan dake faruwa a duniya yanzu haka.
Za a iya samun ƙarin bayanai kan taron ta TRT World Forum 2024 a: www.trtworldforum.com.