Turkiyya tana shirin fara aiki a ɗaya daga wuraren haƙar zinare na Nijar a shekara mai zuwa, kamar yadda Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya sanar, yana mai ƙarawa da cewa ƙasar na bincike a wuraren haƙar zinare a ƙasashen waje.
“Ba tare bai wa duniya da muhalli abin da ya kamace su ba, tattalin arzikin duniya ba zai bunƙasa ba, ba za a tabbatar da tsaro a ɓangaren makamashi ba, sannan ba za a samar da tsaro da kwanciyar hankali ba a duniya,” a cewar Erdogan ranar Juma’a yayin da yake wani jawabi ga Taron Makamashi na Istanbul, wani taron rana ɗaya da aka gudanar a birnin na Turkiyya.
Taron na Makamashi na Istanbul, wanda kamfanin makamashi na Anadolu ya shirya ƙarƙashin Ma’aikatar Makamashi da Ma’adanai da ya mayar da hankali kan taken “Makoma Bai Ɗaya, Manufofi Bai Ɗaya,” ya tattaro shugabannin a harkar makamashi daga faɗin duniya don tunkarar ƙalubalen da ake fuskanta.
Edrodgan ya ce, da bututun iskar gas gudan bakawai, da cibiyoyin gas guda biyu dake kan jiragen ruwa, da kuma mashigu 15, Turkiyya na da damar zama ɗaya daga cibiyoyin hada-hadar makamashi ta duniya.
Turkiyya tana fatan zama ɗaya daga cikin ƙasashe uku dake kan gaba a nahiyar Turai wajen samar da makamashi da ba ya gurɓata muhalli, tare da zama ɗaya daga ƙasashe tara dake kan gana a duniya daga yanzu zuwa 2025, kamar yadda ya bayyana.
Yana bayyana cewa burin Turkiyya shi ne ta kai matsayin samar da megawat 20,000 daga makamashin nukiliya daga nan zuwa 2050. Erdogan ya ce “Da zarar ta fara aiki, Cibiyar Makamashin Nukiliya ta Akkuyu za ta samar da kaso 10% na lantarkin da ake buƙata a Turkiyya, kuma ta kare sakin hayaƙi mai gurɓata muhalli da ya kai tan miliyan 35.”
Nasarorin makamashi
Da yake jaddada cewa a wannan makon ne aka shiga rana ta 1000 ta yaƙin Rasha-Ukraine, lamarin da ya tursasa Turai sake nazarin samar da makamashinta, Erdogan ya yi ƙarin haske kan hatsarin dogaro kan ƙasashen waje don samun makamashi.
Sakamakon daidaitacciyar alaƙa da Turkiyya ke da ita da dukkan ɓangarorin biyu da ke yaƙi, Turkiyya na daya daga kasashen da suka tsaya da kafarsu a lokacin da aka shiga mawuyacin hali saboda yakin, in ji Erdogan.
Turkiyya ta samar da kayan zamani da ke cikin mafiya kyau a duniya da ke nema da haƙar albarkatun mai, da suka haɗa da jiragen ruwa huɗu na haƙar mai da jiragen binciken mai a teku biyu, da jiragen da ke kawo agaji, kamar yadda Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya rawaito Erdogan na fadin hakan.
Waɗannan muhimman kayayyaki sun bayar da dama wajen gano matattarar albarkatun gas mafi girma a tarihin Turkiyya da aka samu a tekun Bahar Maliya shekaru huɗu da suka gabata. A 2023, al’ummar Turkiyya sun fara amfani da gas ɗin da aka samu a ƙarƙashin teku da zurfin mita 4,000 in ji Erdogan.
Ƙaruwar yawan gas da ake fitarwa kullum
Erdogan ya kuma bayyana shirye-shiryen faɗaɗa fitar da gas ɗin ta hanyar fara haƙar wata rijiyar, wadda ake sa ran za ta ƙara yawan gas ɗin da ake fitarwa kullum zuwa kubikmita miliyan 20 kowacce rana nan da 2026 – adadin da zai biya buƙatar rabin gidajen Turkiyya.
Ƙoƙarin da Turkiyya ke yi ya tsallake iyakokinta. Jirgin ruwan neman albarkatun mai na Oruc Reis ya fara neman mai a cibiyoyi uku a gaɓar tekun Somalia, hakan na bayyana burin ƙasar kan ayyukan makamashi a duniya.
Dangane da wuraren haƙar mai kuwa, Erdogan ya yi nuni ga rijiyar man fetur ta Gabar, ɗaya daga cikin cibiyoyin man Turkiyya, inda Turkiyya ta gano man fetur mafi yawa.
A yanzu a kowacce rana ana fitar da sama da gangar danyen mai dubu 57,000, inda jimillar man cikin gida da na waje ya haura ganga dubu 155,000 a kullum. Tare da man da aka gano kwanan nan a Sirnak, Hakkari, da Van, Turkiyya na ci gaba da samun ƙarin matattarar makamashin da za ta dinga samarwa da adanawa.