Wannan ce ziyarar Fidan ta farko zuwa China a matsayin ministan harkokin waje, mukamin da ya hau a watan Yulin bara. . /Hoto: AA

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya ce Turkiyya da China na taka muhimmiyar rawa wajen kare ayyukan jigilar kayayyaki a duniya.

Da yake jawabi a Beijing a ranar Litinin, wadda ya ziyarta bayan gayyatar da takwaransa na kasar Wang Yi ya yi masa, Fidan ya yi nuni da matsayin China kasa ta biyu mafi karfin tattalina arziki a duniya, da kuma irin gudunmawar da take bayarwa don habakar tattalin arziki a duniya.

Ya kuma yi karin haske kan karfin samar da kayayyaki da Turkiyya ke da shi, yawan matasa, kayan more rayuwa, zama laiyar siyasaa ikon fitarda kayayaki.

A yayin da yake yin jawabinsa kan alakar Turkiyya-China a duniya da ke sauyawa kuma China take tsakiya, Fidan ya tabo batun 'Trans-Caspian East-West Middle Corridor Initiative', wani aikin hanyar kasuwanci da zai tashi daga Turkiyya zuwa China, ya bi ta Caucasusu, Tekun Caspian da Tsakiyar Asiya, daura da aikin hanya na Belt na China.

Shirin Hanyar Tsakiya

Fidan ya yi tsokaci da cewa aikin wanda ake kira 'Middle Corridor', na da nisan kilomita 2,000 ta hanyar mota, bai kan nisan hanyar kan teku ba ta tsakanin Turai da Asiya, wanda ke rage tsayin tafiya na kwanaki 15.

Ya kuma jaddada cewa Middle Corroidor' na alfanu mai dorewa ga samun damar isa ga tekunan Bahar Maliya da Bayar Rum cikin sauri, da ma wasu yankuna na Turai da Afirka.

Sannan Fidan ya yi nuni ga yarjejeniyar fahimtar juna da Turkiyya da China suka sanya hannu a kai a 2015 don hadin kan bangarori da ayyukan guda biyu.

Da yake bayyana muhimmancin hade hanyar 'Middle Corridor' da Hanyar China, musamman duba da cewar ana ci gaba da rikici tsakanin Rasha da Ukraine, da kuma hare-haren Isra'ila da Gaza, yana mai cewa aikin ya sake samun muhimmanci sabowa karuwar barazana a yankin.

Fidan ya zayyana muhimmancin samun hadaka tsakanin aikin 'Middle Corridor' da sauran ayyuka kamar na Cigaban Hanya da ya faro daga Basra a kudancin Iraki zuwa arewacin Turkiyya.

Ya kuma ce wannan zai iya hade manyan masu karfin tattalin arziki na Eurosia don cigaba da hadin kan juna.

Ya kawo yarjejeniyar LKungiyar Fito ta Turkiyya da ta kulla da kasashen Turai, d akuma irin damarmakin da ta bayar ga kngiyoyi kamar irin su BRICS.

Ya ce a mako mai zuwa zai halarci taron BRICS a Rasha, inda ya bayyana goyon bayan Ankara ga hadin kai da cimma yarjejeniya tsakanin kasahe da dama a Asiya da Afirka.

Alakar Turkiyya-China

Fidan ya yi karin haske kan dadaddiyar alakar tarihi da al'adu tsakanin tsakanin Turkiyya da China wadanda suke kara inganta alakar, abin da ya kira "Manyan sakafa guda biyu".

Ya jaddada cewar wannan cudanya na assasa babban tushe mai dorewa na hadin kansu, yana mai bayyana mu'amalar kasuwanci da al'adu da Hanyar Silk ta samar a tsakaninsu.

Ya yi tsokaci da cewa Daular Usmaniyya ta tura jakadu da dama zuwa China, sannan da kai bindigin daular, wanda ke nufin "AIka Fahasar Kere-Kere" a wancan lokacin.

Da yake bayyana gamsuwa da cigaba cikin hanzari da ake samu na alakar kasashen biyu, Fidan ya ce wannan hadin kan ya ginu a kan tubalin karfe.

A lokacin da yake bayyana yadda a 2010 aka bayyana alakar kasashen biyu a matsayin 'hadin kai na dabara', Fidan ya yi nuni da niyyar dukkan bangarorin biyu don fadada wannan hadin kan..

China: Babbar kawar kasuwancin Turkiyya a Asiya

Ya bayyana ziyarar da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya kai China a 2019, da kuma muimmancin hadin kan, a yayin ganawa da takwaransa na China Xi Jinping a Samarkand a watan Satumba, 2022.

Fidan ya ci gaba da cewa China ce babbar kawar kasuwancin Turkiyya Asiya, kuma ta uku mafi girma a duniya, inda jarin kasuwanci a tsakaninsu ya haura dala biliyan 48 a 2023, adadi mafi yawa a tarihi.

Ya kuma bayyana yadda ake da rashin daidaito a kasuwancin kasasen biyu inda China ta fi amfana, ya kuma bukaci da a lalubo sabbin hanyoyin da za a samu daidaiton amfana da kasuwancin a tsakaninsu.

Ministan Harkokin Wajen na Turkiyya ya kuma yi karin haske kan babbar rawar da China ke taka wa wajen zuba jari na kai tsaye a tattalin arzikin kawancen, inda ya ce Turkiyya na samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari na kasashen waje.

"Matsayin Turkiyya a yankin, tare da kawnacenmu na kasuwanci mai yawa, na bayar da hanyar haduwa da masu sayen kayayyaki kusan biliyan 1.5 cikin sauki kuma kyau, wanda kayan da za a sayar ya kai na dala tiriliyan 28, tun daga Turai zuwa Gabas ta Tsakiya, Arewacin Afirka da Tsakiyar Asiya.

"Duk wadannan na cikin nisan da bai wuce na tafiyar awanni hudu ba." in ji Fidan.

Ya kara da cewa Turkiyya na taka muhimmiyar rawa wajen magance kalubalen da ake fuskanta a duniya, tare da manufofin kasashen waje da ke haifar da ɗa mai ido, kamar dai irin na China.

Rikicin Jinkai a Rafah

Fidan ya jaddada cewa a yayinda Falasdinawa suka dauki tsawon lokaci suna shan wahala, lamarin ya munana matuka bayan 7 ga Oktoba.

"An taba bayyana Gaza a matsayin budadden gidan kurkuku mafi girma a duniya. A yanzu ta zama makarta mafi girma a duniya. A yau babu wani waje a Gaza da za a iya cewa yana da tsaro."

Ya kara da cewa "Rikicin jinkai da ke afkuwa a kan idanuwanmu ya munana bayan da Isra'ila ta fara kai hare-hare Rafah."

Fidan ya ce tun bayan 7 ga Oktoban bara Turkiyya na ta kokarin ganin an tsagaita wuta a Gaza, hana rikicin yaduwa a dukkan yankin da tabbatar da ba a samu cikas ba wajen kai kayan agaji ga Falasdinawa..

Ya ci gaba da cewa Ankara, kamar Beijing ta bayyana wajabcin tabbatar da ganin an samar da 'yantacciyar kasar Falasdinu da ke da babban birni a Jerusalem, duba ga iyakokin da aka fitar a 1967 a karkashin kokarin warware rikicin ta hanyar kafa kasashe biyu.

Game da rikicin Rasha da Ukraine kuma. Fidan ya ce ana ci gaba da aiki da hanyoyin diplomasiyya don dawo da zaman lafiya.

Ya zayyana cewa "Kawo karshen rikicin Rasha-Ukraine ta hanyar tsagaita wuta da tabbatar da yarjejeniyar zaman lafiya na daga cikin manufofin kasashen waje da Turkiyya ke baiwa fifiko."

Terror activities, peace efforts in region

Fidan ya kuma bayyana muhimmancin yaki da ta'addanci don samar da zaman lafiya da tsaro a yankin, yana mai cewar Ankara na amfani da sojoji, tattalin arziki, diflomasiyya da sauran hanyoyi wajen fatattakar 'yan ta'adda irin su Daesh, PKK, reshenta na Siriya YPG da 'yan ta'addar Fethullah (FETO).

Da yake bayyana PKK da PKK/YPG a matsayin wadanda suka fi tayar da hankali a yankin, kuma suna ci gaba da kai hare-hare Turkiyya ta cikin Siriya, ya ja hankali zuwa ga manufofin 'yan a ware.

A kusan shekaru 40 da suka dauka suna ta'annati, 'yan ta'addar PKK - sun shiga jerin sunayen kungiyoyin ta'adda a Turkiyya, Amurka da Tarayyar Turai - kuma ta yi snaadiyyar mutuwar sama da mutane 40,000 da suka hada da mata, yara da jarirai.

FETO da shugabanta da ke Amurka Fethullah Gulen ne suka yi yunkurin juyin mulkin da aka kawar a ranar 15 ga Yuli, 2015 a Turkiyya, inda aka kashe mutane 252 tare da jikkata wasu 2,734.

Gulen yana zaune a Sylvania da ke Amurka. Tun yunkurin juyin mulkin na 2016, shugabannin Turkiyya sun bukaci da a dawo musu da Gulen zuwa gida, amma mahukntan Amurka sun ki yarda da hakan, suna msu cewar dalilan da Turkiyya suka gabatar ba su gamsar da su ba. Kin dawo da Gulen ya janyo tsama a alakar Turkiyya da Amurka.

Da yake bayyana kokarin Turkiyya na hana Siriya zama matattarar kungiyoyin ta'adda, Fidan ya ce "Mun goyi bayan warware rikicin ta hanya ta siyasa, duga ga daraja da hadin kan Siriya."

Ya kara da cewa "Dadin dadawa, muna aiki don karfafa gwiwar 'yan kasar Siriya su koma kasarsu bisa radin kansu."

Fidan ya yi tsokaci da cewa alakar Turkiyya da kasashen tsakiyar Asiya na daya daga cikin muhimman bangarorin manufofin kasashen wajenta, yana mai kara wa da cewar Ankara na ci gaba da dabbaka manufar fadada hadin kai a bangarori da dama.

Hadin kai da kasashe masu magana da yaren Turkanci

Ya yi nuni da hadin kan kasashe da yawa a karkashin Kungiyar Turkic ta masu magana da yaren Turkanci inda ya ce "ta hanyar kungiyar, muna aiki don karfafa hadin kan yankuna, hanzarta cigaban tattalin arziki da daukaka matsayin siyasa, tattalin arziki da zamantakewa a cikin al'ummarmu."

Fidan ya yi jawabi a ranar Litinin, rana ta farko ta Babban taron Alakar Turkiyya-China a Duniya dake Sauyawa, da aka gudanar a Beijing, China, kamar yadda sanarwar da ma'aikatar ta fitar.

A Beijing, ya gana da Chen Wenqing, mamban Ofishin Jam'iyyar Siyasa ta Kwaminisanci a China (CPC), kuma shugaban kwamitin Siyasa da Harkokin Shari'a, in ji wata sanarwar da ma'aikatar ta sake fitarwa.

Tun da fari a ranar Litinin, ministan harkokin wajen ya ziyarci Beijing don ziyarar aiki ta kwanaki uku, bayan gayyatar da takwaransa na kasar Wang Yi ya yi masa, wanda a watan Yulin bara ya ziyarci Turkiyya.

Wannan ce ziyarar Fidan ta farko zuwa China a matsayin ministan harkokin waje, mukamin da ya hau a watan Yulin bara.

TRT World