Erdogan ya yi jinjina dangane da irin matakin da Majalisar Dokokin Turkiyya ta ɗauka na Allah wadai da irin kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Rafah. / Hoto: AA

Turkiyya ce kaɗai ƙasar da ke fitowa tana mayar da kakkausan martani sakamakon kisan kiyashin da ake yi a Gaza tare da ɗaukar matakai masu tsauri kan Isra’ilar, kamar yadda Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana.

“Mu ne kaɗai ƙasa wadda ta yi martani mai ƙarfi dangane kisan kiyashin da ake yi a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba, tare da ɗaukar matakai masu tsauri kan Isra’ila,” kamar yadda Erdogan ya bayyana a ranar Asabar a wani taron Jam’iyyar AK da ake yi a gundumar Kizilcihamam ta birnin Ankara.

Haka kuma Erdogan ya yi jinjina dangane da irin matakin da Majalisar Dokokin Turkiyya ta ɗauka na Allah wadai da irin kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a Rafah, inda ya ce matakin “yana da matuƙar amfani.”

Game da halin da ake ciki a Falasɗinu, ya ce Turkiyya ta aika da sama da tan dubu 55 na agajin jin kai zuwa yankin.

Zargin kisan kiyashi a Kotun Duniya

A ranar 26 ga watan Mayu, Isra'ila ta kai wani hari ta sama kan sansanin 'yan gudun hijira da ke Rafah, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 45, galibi mata da kananan yara.

Tun a ranar 7 ga watan Oktoba Isra'ila ke ci gaba da kai munanan hare-hare kan Gaza, duk da wani kuduri da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi na neman tsagaita wuta cikin gaggawa.

Kimanin Falasdinawa 36,300 ne aka kashe tun daga lokacin a Gaza, mafi yawansu mata da yara ne, yayin da wasu sama da 82,000 suka jikkata, a cewar hukumomin lafiya na yankin.

Kusan watanni takwas da soma yaƙin Isra'ila, wurare da dama a Gaza sun zama kango a daidai lokacin da ake fuskantar cikas wurin kai abinci yankin, da ruwa mai tsafta, da magunguna.

Ana tuhumar Isra'ila da aikata kisan kiyashi a Kotun Duniya, wanda a hukuncin da ta yanke na baya-bayan ta bayar da umarni ga Isra’ila kan ta dakatar da kai hare-hare Rafah, wanda wuri ne da Falasdinawa sama da miliyan guda suka nemi mafaka daga yakin kafin a mamaye ta a ranar 6 ga watan Mayu.

TRT World