Shugaba  Erdogan  ya kuma yi alkawarin sanyaya zukatan wadanda girgizar ta rutsa da su/Photo AA

Shugaban kasar Türkiye Recep Tayyip Erdogan ya yi alkawarin sake gina yankunan kudancin kasar da girgizar kasa ta ruguza a watan da ya gabata.

“Manufarmu ita ce mu sake gina yankin da girgizar kasar ta afku”, in ji Shugaba Recep Tayyip Erdogan, a yayin taron bude-baki da ya yi a Istanbul tare da wadanda girgizar ta rutsa da su.

Shugaban ya kuma ce Türkiye na da manufar gina isassun gidaje nan da shekara guda domin biyan bukatar matsugunai ga wadanda girgizar kasar ta raba da gidajensu.

Ya kara da cewar za a samar da gidaje 650,000 a shekara guda inda za a fara da gina gidaje 319,000.

Shugaban ya kuma yi alkawarin sanyaya zukatan wadanda girgizar ta rutsa da su.

A ranar 6 ga Fabrairu ne girgizar kasa masu karfin awo 7.7 da 7.6 suka afku a larduna 11 na Türkiye da suka hada da Adana da Adiyaman da Diyarbakir da Elazig da Hatay da Gaziantep da Kahramanmaras da Kilis da Malatya da Osmaniye da Sanliurfa.

Girgizar kasar ta shafi sama da mutum miliyan 13.5 a Türkiye.

AA