Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gana da takwaransa na Kongo Denis Sassou Nguesso a gefen taron BRICS wanda aka gudanar a birnin Kazan na Rasha a ranar Alhamis.
Tattaunawar ta kasance ta sirri a tsakanin shugabannin.
Ministan Makamashi da Albarkatu Alparslan Bayraktar da babban mai bai wa shugaban Turkiyya shawara kan tsare-tsaren ƙasashen waje da tsaro, Akif Cagatay Kilic na daga cikin waɗanda suka halarci tattaunawar.
TRT Afrika