A shekarar 1997 aka kafa kawancen D-8 da manufar habaka tattalin arziki da dangantaka, / Hoto: AA Archive

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya shirya halartar taron Ƙungiyar D-8 a Alkahira babban birnin Masar.

Ministan Kasuwanci na Turkiyya Omer Bolat da Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya Ibrahim Kalin da Daraktan Sadarwa Fahrettin Altun da Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara Kan Manufofin Kasashen Waje da Tsaro Akif Cagatay Kilic na daga wadanda za su raka Shugaba Erdogan zuwa taron a ranar ALhamis din nan.

Ana sa ran taron zai tattauna kan hanyoyin habaka alakar tattalin arziki tsakanin kasashen, kuma za a yi zama na musamman kan Falasdinu da Lebanon.

A shekarar 1997 a Turkiyya aka kafa kawancen D-8 da manufar habaka tattalin arziki da dangantaka.

A sanarwar da aka fitar, Ma'aikatar Harkokin Wajen Masar ta yi karin haske kan muhimmancin taron D-8, wanda ya kunshi kasashen Turkiyya da Nijeriya da Masar da Pakistan da Iran da Indonesia da Malaysia da kuma Bangaladash.

Kalubalen yankuna

Ministan Harkokin Wajen Masar Badr Abdelatty ya halarci taron Majalisar Ministocin Kawancen karo na 21, wanda wani bangare ne na shirye-shiryen taron karo na 11.

Taron ya mayar da hankali kan al'amuran da ke faruwa a yankunansu da ma duniya baki daya.

"Lokacin gudanar da taron na da muhimmanci, ya zo daidai da lokacin da ake fuskantar matsin lambar tattalina arziki a yankuna da ma a matakin kasa da kasa," in ji Abdelatty.

Ya kuma bayyana tasirin wadannan abubuwa da ke faruwa kan kasashe masu tasowa, musamman yakin Isra'ila a Gaza da mummunan sakamakonsa, ciki har da lalata gine-gine.

Ya yi nuni ga abubuwan da Isra'ila ke yi a Gaza da Siriya da Lebanon, yana mai cewar karya dokokin kasa da kasa da Isra'ila ke yi ne ya sanya Masar bayar da shawarar a sadaukar da zaman ga Gaza da Siriya da Lebanon.

Ministan na Masar ya kuma sake jadda muhimmancin hadin kai a tsakanin kasashen, da samar da sabbin damarmakin tattalin arziki da hadin kan kasuwanci da bunkasa shigar 'yan kasuwa don zuba jari da shigar da matasa harkokin jagoranci.

Ganawar Ministocin Harkokin Waje

Tun da fari, an fara gudanar da Taron Majalisar Ministoci a sabon Babban Birnin Masar, inda Abdeltty ya jagoranci zaman.

Taron ya hada da Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan da takwaransa na Iran Abbas Araghchi.

A farkon makon na kuma aka gudanar da taron kwamishinonin D-8 a Alkahira don shirya gudanar da wannan taron.

Taron na ranar Alhamis na da taken "Zuba Jari Kan Matasa da Tallafa wa Kanana da Matsakaitan Sana'o'i da Sauya Fasalin Tattalin Arzikin Gobe."

TRT Afrika