Ana bukatar dabaru na matsakaici da dogon zango don yaki da labaran karya a zamanin da gaskiya ta yi wahala. In ji Daraktan Sadarwa na Turkiye, Fahrettin Altun, a wajen manema labarai bayan Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi ta amince da wani kudiri kan yaki da labaran karya da Kyamar Musulunci.
Altun ya kuma ce, wannan kudiri na İstanbul, an amince da shi a lokacin da kasashe suke gwagwarmayar yaki da Kyamar Musulunci.
Ya kara da cewa “A Kudirin İstanbul, mun samar da kwararan matakai don karfafa hadin kan kasashen Musulmi wajen yaki da labaran karya.”
Ya ci gaba da cewa, “A wannan gaba, mun samar da manufa ta bai daya game da wayar da kan jama’a su fahimci kafafan ya da labarai da cigaban fayyace gaskiya tare da madogarar shari’a.”
A yayin taron na kwanaki biyu da aka yi a İstanbul, Ministoci da manyan wakilan gwamnatoci daga kasashe 57 sun tattauna batutuwa da dama suna neman hadin kai a bangaren sadarwa, kafafan yada labarai da sanarwa a kasashen Musulmi.
An gudanar da taron da taken “Yaki da Yada Labaran Karya da Kyamar Musulunci a Zamanin Da Gaskiya Ta Yi Karanci”, na da manufar fadawa da karfafa hadin kai a tsakanin kasashen Musulmi a fagen yada labarai da sadarwa.
Ya kuma ce, “Mun bayyana irin barazana da labaran karya ke janyowa ga tsaron daidaikun mutane da kasashe, al’umar Musulmi da marasa rinjayea duniya.”
Ya kuma jaddada kudirin OIC ga bukatun Falasdinawa, inda ya ce kasashe mambobi sun amince su kara kaimi a duniya wajen nuna mata “gaskiya da bacin ran Falasdinawa don a kalubalanci farfagandar Isra’ila”.
Haka zalika wannan kudiri ya kuma kunshi bayyana muhimmancin tallafawa ‘yan gudun hijira da kasashen da suka karbe su, kira na a wayar da kai game da nuna wariyar da ake nunawa ‘yan Afirka.
A Kundin İstanbul, mambobin sun jaddada cewa duniyar Musulunci na adawa da duk wani nau’i na nuna wariya, tsaurin ra’ayi, wanke kwakwalen mutane da ta’addanci, in ji Altun.
Altun ya kuma kara da cewa, sun yanke hukuncin samar da wata kafa ta kasa da kasakarkashin OIC do yada irin aiyukan da kasashe mambobin Kungiyar ke yi. ,Ya kara da cewa, “A karkashin Kungiyar, mun yanke shawarar samar da wata taswira ta karkashin Babbar Sakatariya, a samar da tasha ta kasa da kasa da kuma daukar nauyinta.”
A wajen babban taron, wakilin Saudiyya ya mika ragamar jagoranci ga Turkiye don shugabantar Taron Ministocin Yada Labarai na Kungiyar.
Altun ya ce, Azabaijan ce za ta karbi bakuncin taron ministocin sadarwa na nan gaba.