Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce ba za a taba "iya kare wulakanta Alkur'ani da sunan 'yancin fadin albarkacin baki ba" kuma hakan yana kawo cikas ga "dorewar zaman lafiya da zamantakewa", kamar yadda ya bayyana yayin da yake magana da wakilan wata kungiyar addinin Musulunci ta Amurka [USCMO].
Erdogan ya bukaci wakilan a ranar Laraba da su shaida wa majalisar dokokin Amurka da sauran cibiyoyin siyasa na kasar hadarin da ke tattare da sanya karan-tsana a kan addinin Musulunci yayin da yake ganawa da su a fadar shugaban kasa a birnin Ankara.
"Zan so na bayyana godiyata kan aikinku da hadin kai dangane da girgizar kasar ranar 6 ga watan Fabrairun," in ji shi, wato yana magana ne kan batun munanan girgizar kasa biyu a lardin Kahramanmaras da ke kudancin kasar.
Shugaban ya kuma ce al'ummar Musulmin Amurka sun bayar da gudunmawar dala miliyan 100 ga mutanen da girgizar kasar ta shafa kuma hakan ya nuna yadda kan Musulmi yake a hade.
Labari mai alaka: Turkiyya ba za ta lamunci kona Alkur’ani ba: Erdogan
"Al'ummarmu ta yi Allah wadai da karan-tsanar da ake nuna wa Musulunci da tsangwama da kyama, kuma hadin kai yana da muhimmanci wajen yaki da wannan barazana," a cewarsa.
Da yake magana kan babban aikin da kungiyar take yi na wayar da kan jama'a game da adddinin Musulunci bisa ginshikin hakuri da juna da 'yan uwantaka, Erdogan ya ce: "Karfinku a matsayin kungiyar Musulunci a Amurka ya zama misali ga duka Musulman duniya kuma hakan ya kasance abin da ke karfafa gwiwa."
'Laifin kiyayya da dabbanci'
"Abin da suke cewa a kowane lokaci shi ne ba sa goyon bayan wulakanta Alkur'ani a Turai a "karkashin 'yancin fadin albarkacin baki," in ji shi: "Wannan a fili yake laifin kiyayya ne kuma dabbanci ne."
"Muna gani a kowane lokaci wadanda suke kawar da kai daga masu wulakanta addinin Musulunci," a cewarsa.
"An fara samun ci-gaba bayan Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya da Hukumar Kare Hakkin Dan Adam sun yi wani kudiri cewa wulakanta littafai masu tsarki taka doka ne," kamar yadda ya bayyana wa wakilan kungiyar USCMO.
"Tabbas ya kamata su tabbatar cewa ana aiki da wadannan matakan a zahiri. A matsayinmu na Turkiyya, muna ci gaba da kira ga kasashen da abin ya shafa da su dauki matakan da suka dace kan wadanda suke aikata wadannan laifukan kiyayya."
Erdogan ya yi kira ga wakilan da su wayar da kan 'yan siyasa game da hadarin dora karan-tsana a kan addinin Musulunci.
"Da yawanku kuna da damar ganin 'yan siyasa a Amurka. Kuna taka muhimmiyar rawa dangane da dorewar zaman lafiya da zamantakewa. Kuna da wakilai a gwamnatin tarayya da kananan hukumomi.
Ta hanyar amfani da wannan iko, za ku iya sanar da duka 'yan siyasa musamman a Majalisar Dokokin Amurka cewa ba za a taba iya kare wulakanta Alkur'ani ana fakewa da 'yancin fadin albarkacin baki ba," a cewar Shugaba Erdogan.
Ya kara da cewa: "Na yi amannar cewa goyon bayanku zai yi amfani wajen dakushe kaifin kiyayyar da ke nuna Turkiyya. Ina kuma sa ran gudunmawarku kan bayyana gaskiya kan kungiyoyin 'yan ta'adda na PKK da PYD da YPG da kuma FETO ga al'ummar Amurka."
'Nasarar zabe mai cike da tarihi'
Sakatare Janar na Kungiyar USCMO Oussama Jammal ya bayyana godiya da jin dadinsa bisa ganawa da Erdogan.
"Mun zo nan ne a yau don mu taya ka murna. Ka yi nasara a zabe mai cike da tarihi," in ji Jammal.
"Wannan nasarar ba nasara ce taka kai kadai ba, ko kuma ta Turkiyya. Wannan babbar nasara ce ga al'ummar Musulmin duniya gaba daya."