Fidan ya yi jawabi ga manema labarai ranar Asabar a Gidan Turkiyya wato Turkish House da ke New York bayan kammala Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78. / Hoto: AA

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya nuna damuwa game da karuwar nuna wariya da kyama ga Musulmai a Turai, yana mai cewa "hare-haren da ake kai wa littafinmu mai tsarki sun zama annoba."

Fidan ya yi jawabi ga manema labarai ranar Asabar a Gidan Turkiyya wato Turkish House da ke New York bayan kammala Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78.

A yayin da yake cewa duniya tana fuskantar sauyi kan zaman lafiya da walwala, babban jami'in diflomasiyyar na Turkiyya ya ce akwai bukatar Muslmai su hada kansu domin tabbatar da sauyi na gari.

"Ya kamata a wanzar da shiri mai hangen nesa irin Alliance of Civilization ba tare da an yi watsi da makasudinsa ba," in ji shi.

An kafa shirin na United Nations Alliance of Civilization (UNAOC) a 2005 ta hanyar gamayya tsakanin Turkiyya da Sifaniya, wanda ake gudanar da shi karkashin kulawar Majalisar Dinkin Duniya.

Ministan Harkokin Waje Hakan Fidan ya gana da takwaransa na Sifaniya Jose Manuel Albares da Babban Wakilin shirin na United Nations Alliance of Civilizations (UNAOC), Miguel Angel Moratinos, lokacin Babban Taron MDD karo na 78 a New York, inda suka tattauna kan yadda za a shawo kan kyamar Musulunci.

Fidan ya yi tsokaci game da muhimmancin taron, yana mai cewa, "Daukar mataki game da nuna kyama a kan Musulunci na cikin ajandar taron da muka yi".

TRT World