Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yarda ya mika dadaddiyar bukatar Sweden ta neman shiga NATO ga Majalisar Dokokin kasarsa, don neman saka su a gaba su amince da bukatar Turkiyya ta yaki da ta’addanci da kuma shiga Tarayyar Turai.
An mika bukatar Seden ta neman zama mambar NATO ga majalisar dokokin Turkiyya bayan da Shugaba Erdogan ya bayar da haske kan bukatar Sweden ta shiga kawancen mai kasashe 30.
“Majalisar dokokinmu za ta bi matakan da aka dauka kuma za ta yanke hukuncin da ya dace duba ga bukatar kasarmu,” in ji Shugaba Erdogan, bayan da Sakatare Janar na NATO ya bayyana wa duniya azamar Turkiyya a wajen taron Vilnius a makon da ya gabata.
Bayan ganawar da Shugaba Erdogan ya yi da Firaministan Sweden Ulf Kristersson da shugaban NATO, Erdogan ya nuna alamun bayar da goyon baya ga bukatar Sweden, idan su ma za su samu goyon bayanta a bukatarsu ta shiga Tarayyar Turai, cire biza tsakaninsu sannan su sabunta dabarun tsaro na hadin gwiwa da Ankara.
Babban dalilin da ya sanya aka dauki tsawon shekara guda Sweden na jiran amincewar Turkiyya, abu ne da ya shafi wasu abubuwa da ake yi a Sweden, wanda suke janyo nuna kyama ga Musulunci, da kuma ayyukan magoya bayan PKK.
Duk da tabbacin da gwamnatin Sweden ta bayar, a bayyana yake karara ta gaza daukar matakin hana ayyukan nuna kyama ga Musulunci a kasar.
A wani lamari da ake kallon shi ma na tsokanar fada ne, ‘yan sanda a Sweden sun bayar da izinin wulakanta Alkur’ani mai tsarki a wajen ofishin jakadancin Iraki da ke Stockholm a ranar Alhamis din makon da ya gabata.
Mutane biyu ne suka shirya izgilancin da suka hada da Salwan Momika, wanda yana cikin wanda aka yi a lokacin Sallar Layya.
Mutanen da ransu ya baci a Bagadaza sun yi tururuwa zuwa ofishin jakadancin Sweden tare da gudanar da zanga-zangar nuna adawa da kona Alkur’ani Mai Tsarki.
A lokacin da ake ci gaba da nuna bacin rai a kasashen Musulmai, yadda Sweden ta ki daukar matakin magance nuna kyamar Musulunci a kasar zai iya janyo mata tarnaki ga bukatarta ta shiga Kawancen NATO a nan kusa, inda ya zuwa yanzu kasar ta gaza gamsar da Turkiyya kan cika sharuddan da Ankara ta gindaya.
Ga yadda wadannan abubuwa da ke faruwa za su iya bata lamarin.
Yaki da nuna kyamar Musulunci
Har ya zuwa farkon watan Janairu, damuwar Ankara game da bukatar Sweden ta shiga NATO ta shafi barin ayyukan magoya bayan PKK da ke kasar da yadda ake ba su damar shirya tarukan nuna adawa da Turkiyya, da kuma yadda Sweden din ta ki daukar matakan hana hakan.
Masu shuga zanga-zangar nuna adawa da Turkiyya na yawan yin kalamai na cin fuska kamar su kona tutar Turkiyya da hotunan Shugaba Erdogan.
Ba a gama da wancan ba kuma sai ga batun nuna adawa da Musulmai ya bayyana, lamarin da ya zama tamkar tsokanar Turkiyya da duniyar Musulunci a bayyane.
Da fari dai, wani sanannen mai nuna kyama ga Musulunci kuma mai tsaurin ra’ayin siyasa, Rasmus Paludan ya kona Alkur’ani Mai tsarki a watan Janairu a gaban ofishin jakadancin Turkiyya da ke Sweden.
Na biyu kuma shi ne yadda aka sake kona Alkur’ani Mai Tsarki a kasar a ranar Babbar Sallah da Musulmai a karshen watan Yuni – inda wani da ake kira Salwan Momika ya yi aika-aikar a gaban Babban Masallacin Stockholm.
Gwamnatin Sweden ta soki wannan abu inda ta kira shi ‘Nuna kyama ga Musulunci’ bayan kiran da Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmai (OIC) ta yi.
Amma kuma, izinin da aka bayar a ranar Alhamis na shirin kona Alkur’ani a wajen ofishin jakadancin Iraki a Stockholm ya sake kawo shakku kan alkawarin da Sweden ta yi na biyan bukatu da sharuddan da Ankara ta gindaya mata kan yaki da masu nuna kyama ga Musulunci.
Ana bai wa irin wadannan aika-aika kariya da sunan ‘yancin bayyana ra’ayi.
Nagihan Haliloglu, Farfesa a sashen nazarin dan adam a Jami’ar Ibn Haldun da ke Istanbul, ya shaida wa TRT World cewa Sweden na amfani da batun ‘yancin bayyana ra’ayi don jan hankalin Amurka a sauran kasashen Turai mambobin NATO.
Amma kuma Haliloglu ya kara da cewa “Yammacin Turai a hankali na fahimtar cewa amfani da ‘yancin bayyana ra’ayi wajen nuna kyama ga Musulmai abu ne da zai daina tasiri nan da wani lokaci.”
Hungary, wacce ita ma mamba ce ta NATO, ta kulla cikakkiyar yarjejeniya da Turkiyya kan batun Sweden ta zama mambar Kawancen NATO idan ta magance nuna kyama ga Musulunci da Turkiyya.
Kafin Shugaba Erdogan ya hau dokin na ki, Hungary ta taba hana kasashen Scandinavian shiga Kawancen NATO. Kasashen Turai da dama tare da Amurka sun soki yadda aka kona Alkur’ani Mai Tsarki.
Sakamakon matsin lamba daga kowanne bangare, Sweden ta fara binciken nuna laifin tsana kan dan kasar Iraki mai mummunan hali da ya kona Alkur’ani Mai Tsarki.
Mai magana da yawun Tarayyar Turai kan harkokin kasashen waje da manufofin tsaro, Nabila Massrali, ta soki wannan aika-aika, inda take cewa “Kona Alkur’ani ko wani littafi Mai tsarki laifi ne kuma nuna rashin girmmawa ne da tsokana.
Bayyana nuna wariya da kyamar baki da nuna kin amincewa da ke kama da wannan ba su da wajen zama a Turai.”
Yaki da ta’addanci
Turkiyya ta dade tana yaki da ta’addanci tun kafin Amurka ta bayyana yaki da ta’addanci bayan harin 11 ga Satumba.
Kungiyar PKK ta sha kai hare-haren ta’addanci a Turkiyya tsawon shekaru da dama, tana kashe dubban fararen hula da suka hada da mata da yara kanana. Amurka da Tarayyar Turai sun san ayyukan ta’addanci na PKK ga fararen hula inda suka ayyana kungiyar a matsayin ta ta’adda.
Kungiyar na ci gaba da amfani da wasu kasashen Turai wajen yada farfaganda da daukar mayaka, inda wadanda ta wanke wa kwakwalwa suke shiga yaki a Siriya da Iraki da ma Turkiyya.
Domin jan ra’ayin Ankara, a baya-bayan nan Sweden ta amince da dokar yaki da ta’adddanci, wadda ta sanya da wahala a iya daukar nauyin ta’addanci.
Amma gwamnatin Turkiyya na kallon wannan mataki a matsayin wani ado kuma mara tasiri, har sai kasar ta dakatar da duk wasu ayyuka da kalamai da ake yi na nuna adawa da Turkiyya da Musulmai a kasar wadanda su ne bukatun Ankara na dawo mata da ‘yan ta’adda ta hukunta su.
Tun 2017, Turkiyya tana ta nanata a mika mata ‘yan ta’addar FETO da PKK d suke rayuwa a kasar.
A karon farko na daukar matakin adawa da PKK, Kotun Sweden ta yanke wa wani mamban PKK hukunci saboda samun sa da laifin daukar nauyin kungiyar da kuma safarar miyagun kwayoyi.
Amma kuma a makon da ya gabata Kotun Kolin Sweden ta ki amincewa da dawo da wasu mambobin FETO biyu zuwa Turkiyya inda ta ce bukatar Turkiyya ba ta yi daidai ka’idojin aikata ta’addanci a kasashe biyu ba.
Safarar makamai da ta’addanci
Sweden da Finland sun janye hanin sayar wa da Turkiyya makamai da suka saka wa kamfanoninsu, amma mahukuntan Turkiyya sun ce sai an kara daukar kwararan matakai kan batun yaki da wanzuwar ‘yan ta’addar PKK da ke kasar.
Hanin ya biyo bayan yaki da PKK da Turkiyya ke yi, da ma reshen kungiyar na YPG-SDF/PYD da ke arewacin Siriya da Iraki.
Amurka da kawayenta suna taimaka wa SDF da sunan suna yaki da ‘yan ta’addar Daesh, suna cewa SDF ba su da alaka da PKK inda suke ayyukansu tare.
Yadda Sweden ke kai makamai ga PKK a Siriya ya zama batun tababa tsakanin banrarorin biyu.