Ministan Harkokin Waje Hakan Fidan ya halarci taron Kungiyar Hadin Kan Kasashen Yankin Bahar Rum karo na takwas. /Hoto: AA

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan tare da takwarorinsa na sauran kasashen Musulmai sun gana da babban jami'in diflomasiyyar Sifaniya Jose Manuel Albaresto a Barcelona, don tattaunawa kan matakin da za a dauka da manufar kawo karshen rikicin Gaza, in ji wata sanarwa da Ma'aikatar ta fitar a shafin X.

Fidan da Albaresto tare da sauran ministocin harkokin waje da ke wakiltar taron hadin gwiwa na Kungiyar hadin kan Kasashen Musulmai da Kungiyar hadin Kan Kasashen Larabawa sun kuma tattauna kan matakan da za a dauka don samar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.

Fidan ya tafi Sifaniya don halartar taro karo na takwas na Kungiyar Kasashen Yankin Bahar Rum. Ma'aikatar ta ƙara da cewa an kuma tattauna kan halin tsaka mai wuya da ake ciki saboda rikicin Falasdin da isra'ila da kuma abun da zai biyo bayan yakin.

Ministan harkokin wajen na Turkiyya ya kuma gana da takwaransa na Ailan, Michael Martin a wajen taron.

Kwanaki hudu na ayyukan jin kai a Gaza

A ranar Juma'ar makon da ya gabata ne Qatar da Masar da Amurka suka jagoranci cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na kwanaki hudu don samun damar gudanar da ayyukan jin kai, inda Isra'ila ta dakatar da kai hare-hare Gaza.

A kwanaki biyu na farko na tsagaita wutar, Hamas da Isra'ila sun yi musayar fursunonin yaƙi 'yan Isra'ila 41 da Falasdinawa 78.

A karkashin yarjejeniyar, za a saki fursunonin a matakai daban-daban a tsawon kwanaki hudu.

A ranar 7 ga Oktoba ne Isra'ila ta kaddamar da hare-hare kan Gaza bayan harin da Hamas ta kai mata.

Isra'ila ta kashe Falasdinawa 14,854 da suka hada da yara kanana 6,150 da mata 4,000, kamar yadda jami'an lafiya suka sanar. An bayyana mutuwar 'yan Isra'ila 1,200 a rikicin.

TRT World