Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan da Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken sun gana don tattauna abubuwan da suka faru a Gaza gabanin taron kungiyar tsaro ta NATO a Brussels, kamar yadda Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fada.
Tattaunawar ta zo ne a daidai lokacin da aka tsagaita wuta a Gaza, wanda aka tsawaita daga kwanaki hudu zuwa shida, don ba da damar musayar fursunoni da kuma kai kayan agajin da ake bukata ga Falasdinawa a Gaza.
An tsagaita wutar ne saboda gagarumin farmakin soji da Isra'ila ta kai a Gaza na Falasdinu, tun bayan wani harinba-zata da kungiyar Hamas ta kai a ranar 7 ga watan Oktoba.
Tun daga lokacin ta kashe Falasdinawa sama da 15,000, da suka hada da yara 6,150 da mata 4,000, a cewar hukumomin lafiya a yankin da aka yi wa ƙawanya. Adadin wadanda suka mutu a hukumance na Isra'ila ya kai 1,200.
Batun saka Swedena ƙungiyar NATO
Fidan da Blinken sun kuma tattauna kan tsarin saka Sweden ƙungiyar NATO, in ji ma'aikatar a ranar Talata.
A ranar 16 ga watan Nuwamba, kwamitin harkokin waje na majalisar dokokin Turkiyya ya ɗage nazarin matakin amincewa da kasar Sweden shiga kungiyar NATO.
Don shiga cikin ƙawancen, wanda Sweden ke nema bayan fara yaƙin Rasha da Ukraine, ya zamewa Stockholm dole ta sami amincewar duk mambobin NATO na yanzu, ciki har da Turkiyya, wacce mamba ce ta sama da shekaru 70.
Kasar Turkiyya dai na matsawa mahukuntan kasar Sweden daukar ƙwararan matakai domin magance matsalar tsaro da Ankara ke fuskanta, musamman dangane da tallafawa kungiyar ta'adda ta PKK.
A cikin sama da shekaru 35 da take yi na ta'addanci a kan Turkiyya, PKK - wadda Turkiyya da Amurka da EU da suka sanya a jerin sunayen 'yan ta'adda - ita ce ta yi sanadin mutuwar mutum fiye da 40,000 da suka hada da mata da yara da jarirai.
Ministocin harkokin wajen kungiyar tsaro ta NATO sun hallara a hedkwatar NATO domin tattaunawa kan yakin da ake yi a Ukraine da kuma yankin Gabas ta Tsakiya, da kuma yadda ake ci gaba da gasar manyan tsare-tsare.