Kungiyar FETO da shugabanta mazaunin Amurka Fetullah Gulem ne suka kitsa juyin mulkin da aka daƙile, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 253 da kuma jikkata 2,734. AA

Daga

MURAT SOFUOGLU

Kungiyar FETO da shugabanta mazaunin Amurka Fetullah Gulem ne suka kitsa juyin mulkin da aka daƙile, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 253 da kuma jikkata 2,734.

Yayin da Turkiyya ke tunawa da cika shekaru takwas da yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba, har yanzu Ankara na jiran Amurka ta miƙa mata wanda ya kitsa harin a kan Dimokuraɗiyyar Turkiyya da al'ummarta ranar 15 ga watan Juli, abin da ya haddasa mutuwar mutane 253 da kuma jikkata fiye da 2,700.

Fetullah Gulem, jagoran kungiyar ƴan'ta'adda ta (FETO) yana gudanar da aikace aikacen kungiyar ta'addancinsa mai yaɗuwa daga gidansa da ke Pennsylvania tun shekarar 1999.

Duk da buƙatu sau da dama da Turkiyya ta gabatar na a taso ƙeyarsa daga Amurka, Washington ba ta miƙa shi ga ƙawarta ta NATO ba, abin da ya ɓata wa Ankara rai kuma yake jawo wa jami'anta da yawa suna saka ayar tambaya dangane da cancantar daɗaɗɗen ƙawancen siyasa da na soji tsakanin kasashen biyu.

Duk da nuna rashin amincewa sau da dama da Turkiyya ta yi, amma Amurka ta ci gaba da bai wa ƙungiyar YPG kariya, wato ƙungiyar PKK reshen Syria, wacce Washington da Ankara tare da EU da NATO suka ayyana a matsayin Kungiyar 'yan'ta'adda.

"FETO a matsayinta ta kungiyar addini mai nasaba da siyasa, wani ɓangare ne da Amurka ke amfani da shi wajen kaddamar da yaƙin sunƙuru a faɗin duniya. Wato ma'ana, wata kungiya ce da take amfani da ƙarfin faɗa-a-ji a madadin Amurka a cikin Turkiyya da kuma faɗin duniya", a cewar Abdullah Agar, wani mai sharhi kan al'amurran sojoji na Turkiyya.

Yayin da Gulem mai wa'azi ne, kuma, bisa ga dukkan alamu, kungiyar ta Gulem ta yi kama da ta addini, a cewar Ager, amma muradansu ba su taƙaita ga addini ba kaɗai; har da siyasa, kuma sun gudanar da al'amurra a yankuna daban daban a faɗin duniya.

"FETO ta bayyana a Turkiyya da sunan Musulunci, amma hidima ta yi wa ƙasashen yamma da Amurka ba a Turkiyya ba kaɗai har ma da wasu ƙasashen masu yawa," Ager ya sheda wa TRT World.

Muhimman kafofi

Idan Amurka ta tisa ƙeyar Gulem zuwa Turkiyya, hakan zai iya zama kawarwa ko gazawa wajen kare ɗan kanzaginta na duniya, abin da zai iya jawo ce-ce-ku-ce cikin harkokin tsaro da na siyasar Washington, sannan ya yi mummunan tasiri kan amincin Amurka.

A cewar Ager, hakan zai yi mummunan tasiri kan sauran 'yan kanzagi kamar YPG/PKK a Syria. A wannan mahangar, an fahimci dalilin da ya saka Amurka ke ci gaba da bai wa FETO kariya.

Sojojin Amurka suna bai wa mambobin YPG horon soja, waɗanda Turkiyya ta ke kallo a matsayin wani reshen PKK ne a Syria. AA ARCHIVE

"A ɗaya bangaren, miƙa wa Turkiyya Gulem da Washington za ta iya yi yana tattare da babbar kasada ta fuskar bankaɗo munanan ayyukan FETO da hulɗoɗinta na duniya. Gabaɗaya dai, idan Gulem ya shiga hannun Ankara, za a kawar da wanzuwar FETO a Turkiyya da a duniya, da kuma shafe ta kwata kwata a doron ƙasa," Ager ya ce.

A lokaci guda, Ager ya yi imanin cewa, irin Musulunci na masu sassaucin ra'ayi da FETO take kira a kai ya zo daidai da irin aƙidun da Amurka da Kasashen yamma ke mara wa baya da hadafin sauya tunanin al'ummomin Musulmi a faɗin duniya, domin hana su tabbatar da ƴantaccen muradunsu na siyasa da tattalin arziƙi.

Sami al Arian, daraktan Cibiyar Musulunci Da Al'amurran Duniya a Jami'ar Sabahatti Zaim ta Istanbul, wanda ya yi nazari a kan kungiyar tsawon shekaru, shi ma yana ganin cewa Washington na ɗaukar ƙungiyar a matsayin wata muhimmiyar kafa da za a iya amfani da ita a hura wa Turkiyya wuta.

Yayin da Amurka ba ta son ɗaukar matsaya da ke nuna goyon baya ƙarara ga ƙungiyar da ta haddasa yunƙurin juyin mulki a ƴan shekarun baya bayan nan a Turkiyya, ƙasa ta biyu mafi yawan sojoji a ƙawancen NATO, amma Washington ta damu da manufofin Turkiyya, waɗanda ke nuna wasu nau'o'in bijire wa manyan kasashen duniya, kamar yadda Arian ya ce

A shekarar 2019, Turkiyya ta sayo jirgin yaƙi samfurin S-400s a wajen Russia bayan Amurka ta ja ƙafa kan buƙatar Ankara kan makamai samfurin patroit. Hakan ya ƙara zaman doya da manja tsakanin ƙawaye biyu na NATO. Haka kuma, Amurka ba ta bai wa Turkiyya jirgin yaƙi samfurin F-35 ba, ta cire shi daga shirin, abin da har ila yau, ya haifar da rashin jituwa.

Haka kuma Turkiyya ta ɗauki mataki na daban a rikicin Ukraine, ta kulla ƙawance mai ƙarfi da Russia domin kawo karshen mummunan yaƙin, saɓanin kasashen yamma.

A baya bayan nan, Turkiyya ta bayyana aniyarta a fili ta shiga ƙawancen kasashen BRICS, wani ƙawancen da ba na kasashen yamma ba, wanda ya samo asali daga ƙasashen ƴan ba ruwanmu na zamanin yaƙin cacar baka. BRICS ta ƙunshi Russia da China da India.

Saɓanin galibin kasashen yamma, Ankara ta goyi bayan gwagwarmayar Palastinawa kan zaluncin Isra'ila a Gaza, tana hulɗa da shugabannin Hamas a fili, kuma tana buƙatar gwamnatin Amurka mai mara wa Isra'ila baya, da ta matsa wa Tel Aviv lamba ta hau teburin tattaunawa tare da Palastinawa.

Shugaban Turkiyya Erdogan ya gana da shugaban kungiyar Hamas Isma'il Haniyeh a Istanbul a watan Afrilu domin tattaunawa kan yadda za a kai tallafin jinƙai zuwa Gaza./Hoto:AA

"Sun yi kokarin sauya manufofin Turkiyya saboda Ankara, a ƴan gwamman shekarun nan, tana ta ƙoƙarin sama wa kanta alƙibla, tabbatar da ƙarin ƴanci wajen ɗaukar mataki da kuma nuna ƙarfin ikonta a yankin, tana ƙoƙarin taka muhimmiyar rawa a batutuwa da dama da suka shafi Amurka, abin da kuma zai iya zama illa ga muradun Amurka Kamar yadda Amurkan ke kallo abun,"a cewar Ager.

Tabbas ana amfani da Gulem ta hanyar hukumomin leƙen asiri, CIA da sauransu a abin da ya shafi matsayin Turkiyya a siyasance, a faɗar Arian. " Sun kasance suna amfani da shi a al'amurra idan akwai babbar hamayya ko bambancin a manufa tsakanin Amurka da Turkiyya."

Matthew Bryza, wani tsohon babban jami'in diflomasiyyar Amurka, ya yi imani cewa cikas da ake samu wajen miƙa wa Turkiyya Gulem yana da nasaba da tsarin shari'ar Amurka mai wuyan sha'ani a maimakon kowane irin mataki na siyasa da Washington ta ɗauka na ba shi kariya.

Amma Bryza ya gaya wa TRT World cewa " akwai fahimta bayyananniya a gwamnatin Amurka cewa akwai hannun Fetullah Gulem a juyin mulki ko ma yana kan shirya juyin mulki."

A wata tsohuwar hira da TRT World, Richard Falk, farfesan dokokin ƙasa da ƙasa, ya bayyana yiwuwar saka hannun Amurka a yunkurin juyin mulkin, yana cewa, wasu alamomi na zahiri sun nuna cewa, masu juyin mulkin, sun samu sahalewar aiwatar da juyin mulkin daga Washington.

A daren 15 ga watan Juli, lokacin da John Kerry, a lokacin shi ne sakataren harkokin kasashen waje, yana Moscow, sai ya fitar da sanarwa yana kiran da a yayyafa wa fitinar ruwa, abin da ya nuna cewa duk yadda aka yi Amurka na da masaniya game da yunƙurin juyin mulkin, a cewar Arian.

"Idan suna sane da da wannan juyin mulkin,ko shakka babu, hakan na nufin akwai haɗin bakinsu," ya ce.

Wani ajiyayyen hoto da aka ɗauka ranar 15 ga watan Juli 2016 yana nuna ƴan ƙasar./Hoto:AA

Turkiyya sun fantsama kan tituna domin mayar da martani kan yunkurin juyin mulki,a kan tankar yaƙi yayin da suka tsayar da motar sojoji mai sulke a titin Vatan da da ke Istanbul, Turkiyya.

Alaƙa da masu fafutukar tabbatar da ƙasar Yahudawa

Haka kuma,Arian ya jawo hankali game da wani muhimmin bangaren, alaƙa mai ƙarfi da Gulem ke da ita da Yahudawa masu kamun ƙafa kan kafa ƙasar Yahudawa da ke Amurka, waɗanda suke da karfi faɗa a ji sasai a kan ƴan siyasar Jam'iyun Democrat da Republican. "Gulem a Amurka yana alaƙanta kansa da kungiyoyi da muradun tabbatar da ƙasar Yahudawa da yawa," Arian ya ce.

Yana cewa FETO tana halarta da kuma shirya tarurruka a Amurka domin ƙara danƙon zumuncinsu da kuma alaƙarsu da Yahudawa.

Ko da shari'ar tisa ƙeyar Gulem, wacce mai wahala da tsayi ce saboda wuyan sha'anin tsarin shari'ar Amurka, ta kankama a wa'adin mulkin Democrat, ko shakka babu Republican za su yi adawa da hakan saboda FETO za ta samu wani a ɗaya bangaren da ke goyon bayan Gulem saboda yiwuwar samun alaƙa da masu fafitikar tabbatar da ƙasar Yahudawa, ya bayyana.

"Za su kawo masa ɗauki. Masu kamun ƙafa don kafa ƙasar Yahudawa za su fara motsa waɗannan mutanen, ko a dama ko hagu, ko Democrat ko Republican ta yin amfani da wannan hanyar, har ma samun fifikon siyasa kan sauran jam'iyun," Farfesan ya faɗa.

A baya, Gulem ya furta lafazin goyon bayan Isra'ila. Alal misali, harin da Isra'ila ta kai kan jiragen ruwan da ke dauke da kayan tallafin jinƙai na ƙasa da ƙasa zuwa Gaza wanda ke da hadarin kawo karshen rufe yankin Falasdinawa da Isra'ila ta yi.

Mummunan harin na Isra'ila ya haifar da mutuwar Turkawa ƴan fafutika guda 10.

Masu kai tallafin jinƙai zuwa Gaza da sun nemi izini daga Isra'ila kafin su kai tallafin ga Falasdinawa, ya gaya wa Wall Street Journal a hirarsa ta farko da wata kafar watsa labarai ta Amurka a 2010,yana bayyana abin da suka aikata da yi wa hukumar Isra'ila karan-tsaye.

Kamun ludayin Gulem a game da Isra'ila yana da fa'ida ga muradun ƴan fafutika kafa ƙasar Yahudawa a yaƙi da suke da burin Palastinawa a cewar Arian. Gwamnatin Isra'ila da buƙatun Yahudawa suna son yin amfani da Gulem a matsayin wani abun matsin lamba kan Turkiyya ta wanke hannu daga kan batun Palastinawa kamar yadda gwamnatin Turkiyya take yi tsawon shekaru ashirin.

Mene ne hadarin Gulem?

A wajen gwamnatin Turkiyya, juyin mulkin 15 ga watan Juli da bai yi nasara ba, wata manuniya ce a fili ta burin shugaban na FETO na karɓar shugabancin ƙasar. "Idan ka yi nazari mai zurfi kan waɗannan burikan, za ga gane cewa bai damu sosai da shugabancin dimokuraɗiyya ba ko shugabanci bisa doka ta hanyar wakiltar jama'a," a faɗar Arian.

“Saboda haka, ko ma mene ne ya sa ya aikata abin da ya aikata, abu ne da yake son ƙwata da ƙarfin tuwo, kuma ya yi ƙoƙarin ƙaƙaba wasu matakai da aƙidu da kuma wasu tunani da yake ta assasawa tsawon shekaru," Farfesan ya bayyana.

TRT World