Gini ne mai ban sha’awa a tsakiyar birnin kuma
A yayin da ka doshi Masallacin Sultan Ahmet, za ka fara shakar kamshin bishiyoyi masu yalwar ganye da ke ciki da wajen masallacin.
Harabarsa ta farko na da girma sosai.
Masallacin na da tsayin mita arba’in da biyar. Haka zalika yana da dogayen hasumiyoyi har guda shida wadanda suke kara masa kyau da kwarjini. Baya ga wadannan hasumiyoyi, kubbar tsakiya ta Masallacin Juma’a na Sultan Ahmet ma na da tsawon mita arba’in da uku.
Baya ga gudanar da ayyukan ibada na yau da kullum, mutane na zama su huta, su shakata a wurin. Akwai ma wurin sassarfa.
Idan ka shiga haraba ta biyu, nan ma dai bishiyoyi masu koren ganye, da furanni masu kamshi za ka tarar na maka maraba.
Sannan ga ado mai daukar hankali da aka yi a jikin bango da katangarsa.
Kana shiga ciki kuma, za ka tabbatar da lallai ka shiga waje na musamman da ba a ko’ina ake samunsa ba.
Ga wasu kayatattun fitulu da ke daukar idanuwa, sannan ga darduma ta musamman launin ja mai ado da aka shimfida.
An yi wa cikin Masallacin adon zayyana da digo-digo launin shudi wanda hakan ya sanya Turawa suke kiran sa da ‘Blue Mosque’. Shi ne Masallaci mai hasumiyoyi shida na farko da aka gina a Turkiya.
A cikin Masallacin an ware waje na musamman ga wadanda suke son yin Sallar farilla ko nafila. Sannan akwai bangaren da kawai masu yawon bude ido ne ke shiga.
Sannan kuma, kasancewarsa a bude ga kowa, idan mata da ba sa daura dankwali suka zo, ana ba su abin rufe kai domin tabbatar da da’a a masallacin da kuma girmama tsarin Musulunci.
Kasancewarsa a gabar mashigar tekun Santanbul, masallacin Juma’a na Sultan Ahmet na kara wa birnin kyau matuka musamman ga masu shiga birnin ta teku.
Muhimmancin masallacin Sultan Ahmet ga raya al’adu da yawon bude ido
Masallacin Sultan Ahmet na daga jerin kayan tarihi da raya al’adu da Majalisar Dinkin Duniya ke bai wa kariya da kulawa ta musamman. Dalili shi ne a shekarar 1985, Hukumar Bunkasa Ilimi, Kimiyya da Raya Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO) ta sanya shi a jerin wuraren tarihi.
Masallacin Sultan Ahmet, wanda ke gundumar Fatih da ke birnin Santanbul, yana daya daga cikin Masallatai mafiya girma da ban mamaki a birnin.
A harabar Masallacin ba wajen ibada kawai ake da shi ba, akwai hubbaren Sarki Sultan Ahmet na I, da wajen wanka na musamman da ake kira da hamam da dai sauransu.
Wannan Masallaci mai dimbin tarihi na kasancewa a bude ga maziyarta na cikin gida da kasashen waje. Kuma ba a karbar ko taro domin shiga.
Ba Musulmai kadai ke shiga Masallacin ba, har wadanda ba Musulmai ba ma na samun damar shiga.
Yadda aka gina masallacin Sultan Ahmet
Tarihin Masallacin Sultan Ahmet na daya daga cikin Masallatan Juma’a mafi girma a Turkiye.
A shekarar 1609 aka fara aikin gina masallacin a zamanin Sarkin Daular Usmaniyya Sultan Ahmed na I.
An gina shi da salon fasahar gini ta Daular Usmaniyya da kuma ta Daular Gabashin Roma wadda ta gabaci daular Usmaniyyar.
Sultan Ahmet ne ya umarci kwararren magini Sedefkar Mehmet da ya gina Masallacin. An dauki kusan shekaru 8 ana aikin. An kamala a shekarar 1617. Jim kadan da kammala gina masallacin, Sultan Ahmed ya rasu.
Bayan kamala aikin ginin, jama’ar Turai sun sanya wa Masallacin sunan ‘Blue Mosque’ wato Shudin Masallaci saboda amfani da launin shudi wajen kawata cikinsa.
Amma a hukumance sunan masallacin shi ‘Masallacin Sultan Ahmet’’ kuma an sa sunan ne domin tunawa da sarkin Daular Usmaniyya da ya gina shi a lokacin mulkinsa. Masallacin na da tsayin kusan mita 45.
Masallacin Sultan Ahmet ya zama mafi girma a Turkiya, musamman ma bayan mayar da Hagia Sophia zuwa gidan adana kayan tarihi a shekarar 1935. To amma yanzu ya koma matsayin na biyu mafi girma bayan da aka sake mayar da Hagia Sophia ya zama masallaci a 2020.
Dalilin da ya sa aka yi wa masallacin hasumiyoyi shida
Akwai ruwayoyi daban-daban na yadda aka yi hasumiyoyin masallacin. Wata ruwaya na cewa sarkin Daular Usmaniyya Ahmet na I ya bukaci kwararren magini Sedefkar Mehmet Aga da ya gina hasumiyar masallacin da zinare wanda a harshen Turkanci ake kira ‘altin’, amma kuma maginin sai ya dauka ana nufin hasumiyoyi guda shida saboda kalmar shida a Turkanci ita ce ‘alti’ kuma tana kamanceceniya sosai wajen furuci da rubutu da kalmar ‘altin’ da ke nufin zinare.
Haka zalika, saboda kasancewar Sarki Sultan Ahmet na I da ya bayar da umarnin gina Masallaicin shi ne sarkin Daular Usmaniyya na 16, sai aka gina wasu kananan kubbobi na karamci guda 16 a masallacin.
Bayan an gama gina Masallacin sai wasu suka fadawa Sarki cewa ai a wannan zamanin Masallacin Ka’aba ne kadai ke da hasumiyoyi shida, a saboda haka yin hasumiyoyi shida a wannan Masallaci ya zama tamkar nuna rashin girmamawa ga Masallacin Makka mai alfarma.
Da Sarki ya ji haka sai ya sanar da magini Sedefkar Mehmet Aga wanda shi kuma nan da nan ya kama hanya zuwa Ka’aba. Bayan shekaru biyu ya dawo