Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya amsa tambayoyin ƴan jarida a yayin da yake kan hanyarsa ta komawa gida daga ƙasar Hungary bayan kammala taro karo na shida na kwamitin hadin gwiwa tsakanin Turkiyya da Hungary.
A ranar Talata Shugaban Turkiyya Erdogan ya nuna alamun cewa ya hango tafiyar Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a yayin da ƙasarsa ke tsaka da ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza.
Shugaban na Turkiyya, wanda ke fafutukar ganin an yi adalci ta hanyoyin shari'a, inda yake burin ganin an kama dukkan masu hannu a kisan ƙare dangin da ake yi da laifukan yaƙi, ya nanata cewa ko da Netanyahu ya bar mulki hakan ba zai sa a wanke shi ba.
Erdogan ya jaddada cewa ba Netanyahu ne kawai zai fuskanci shari'a ba, har ma da duk wanda ke da hannu a zalincin da ake yi a yankin Falasɗinu da aka yi wa ƙawanya.
Shugaba Erdogan ya ziyarci Hungary ne don halartar wani taron diflomasiyya a ranar Litinin, wanda daga bisani aka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar hadin gwiwa mai ƙunshe da batutuwa 17 a tsakanin kasashen biyu, da nufin ɗaukaka alaƙarsu zuwa ga inganta hulɗar abokantaka bisa manyan tsare-tsare.
A yayin ziyarar tasa, Erdogan ya bayyana cewa, baya ga dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu, dangantakar Turkiyya da Tarayyar Turai da ci gaban Ukraine da Gaza na cikin ajandar.
Shigar Sweden NATO
Erdogan ya bayyana cewa ganawar da ya yi da shugaban Amurka Joe Biden ya tattauna kan batun shiga kungiyar NATO a Sweden da kuma sayen jiragen yaƙi na F-16 da Turkiyya ta yi.
Kyakkyawan ci gaba da ake sa ran daga Amurka kan batun F-16 za su ƙara saurin matsayar majalisar dokokin Turkiyya game da kasancewar Sweden a kungiyar NATO.
Ya ƙara da cewa, Turkiyya na fatan kasar Sweden ta cika alkawuran da ta dauka.
Hanyar shigar da hatsi
Dangane da aikin da ake yi na shirin samar da hatsin da ake yi a Tekun Bahar Aswad, Erdogan ya ce akwai bukatar a tabbatar da cewa kasashen Afirka da ke da bukata sun amfana da shi.
Da yake magana kan wata ganawar da zai yi da takwaransa na Rasha Putin, Erdogan ya ce za su ce, "Bari mu yi duk abin da ya kamata don gudanar da aikin hanyar," nan ba da jimawa ba, yana mai bayyana fatansa na ci gaba da shirin.
Dangantakar Turkiyya da EU
Erdogan ya yi magana a kan dangantakar Turkiyya da Tarayyar Turai EU, yana mai cewa akwai buƙatar ƙungiyar ta sake duba matsayin Turkiyya da kyau daga yanzu.
Da yake nanata cewa, ba daidai ba ne a ci gaba da riƙe kasar Turkiyya wadda ta fi sauran kasashe mambobinta, tana jira a bakin ƙofa na tsawon shekaru saboda cikas na siyasa, ya ce: "Ya kamata a ce an riga an tabbatar da cewa Turkiyya na da cikakkiyar damar shiga kungiyar ta EU.
"An shafe shekaru ana jinkiri tare da ba da uzuri daban-daban. Muhimmancin Turkiyya da tasirinta a matsayin ƙasa ya sake bayyana a cikin tsarin da muka samu a cikin 'yan shekarun nan," in ji Erdogan.
Ya yi kira ga kungiyar da ta yi watsi da kuskuren da aka yi na jinkirta zaman Turkiyya mamba ta hanyar ba da uzuri daban-daban.