An samu gagarumin ci gaba a kasuwanci tsakanin Turkiyya da Syria a watan farko na shekarar 2025, inda ƙudaden kayayyakin da Turkiyya ke fitar wa zuwa Syria a duk shekara ya ƙaru da kaso 35.5 cikin 100, inda ya zuwa ranar 25 ga watan Janairu ya kai dala miliyan 219, a cewar ministan harkokin kasuwancin ƙasar Omer Bolat.
A ranar Talata ne, Bolat ya jadadda cewa, sabuwar gwamnatin Syria tana aiki ''ka'in da na'in'' tare da Turkiyya, kana ya nuna kwarin gwiwa game da ci gaban da ake samu a fannin kasuwanci da zuba jari da kuma ƙokarin sake gina ƙasar.
Kazalika minsitan ya bayyana cewa, an ware wasu muhimman kayayyaki kamar abinci da na gine-gine daga cikin waɗanda ake biyan haraji na shiga da fitar da su a lokacin basasa na Syria.
Sai dai, a ranar 11 ga watan Janairu ne sabuwar gwamnatin ta fitar da wasu sauye-sauye, inda ta yi gyara kan tsarin haraji 6,302 a matsayin wani babban sauyi na bai- ɗaya na harajin hukumar kwastan don bunƙasa kudaɗen shiga.
''Yayin da ƙarin biyan haraji kan wasu kayayyaki a arewancin Syria, an samu ragi kan wasu, sannan mun gano wasu rahotannin ƙarya da ke iƙirarin cewa sabuwar gwamantin Syria ta sanya haraji mai yawa kan kayayyakin Turkiya idan aka kwatanta da na ƙasashen Larabawa'' in ji Bolat.
Ya kuma bayyana cewa, an samar da waɗannan sauye-sauyen ne don biyan buƙatun kudaɗe kashewa na al'umma ba wai don Turkiyya ba.
Ƙarfafa dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu
Bolat ya kuma bayyana dadaɗɗen dangantakar kasuwanci da ke tsakanin Turkiyya da Syria, yana mai nuni kan yarjejeniya 'yancin kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu da aka rattaɓa wa hannu a 2007.
Ko da yake an dakatar da wannan yarjejeniyar bayan soma yakin basasa na ƙasar.
''Mun ba da shawarar a sake farfado da wannan yarjejeniyar, kuma Syria ta nuna goyon bayanta game da wannan shawara,'' in ji shi.
Ministan ya kuma kara da cewa, Turkiyya ta gargadi Syria game da illar hauhawar farashin kayayyaki wanda ƙarin harajin kwastam ɗin zai haifar.
“Mun ba da shawarar cewa idan aka rage haraji kan muhimman kayayyakin masarufi hakan zai taimaka wajen dakile hauhawar farashi na kayayyaki, a kan haka Syria ta sanar da cewa za ta rage haraji kan wasu kayayyaki 269 waɗanda suka hada da madara da kwai da fulawa da ƙarafa da kuma robobi,'' in ji Bolat.
A cewar ministan, kayyakin da Turkiyya ta fitar zuwa Syria a shekarar 2023 kafin rugujewar gwamnatin Assad sun kai dala biliyan 2.2, yayin da kuma kayayyakin aka shigo da su daga ƙasar suka kai na dala miliyan 450.
Bolat ya bayyana cewa, a cikin makonni biyu bayan soma aikin sauye- sauyen daga ranar 11 ga watan Janairu, kayayyakin da Turkiyya ta fitar zuwa Syria sun haura na dala miliyan 130, hakan ya nuna ƙarin kaso 33 cikin 100 da aka samu a tsakanin lokacin kaɗai.
Ƙaruwar yawan zirga-zirga kan iyaka
Ministan ya kuma yi ƙarin haske game da harkokin kasuwanci da ke gudana a kan iyakokin kasashen biyu, inda ya bayyana cewa, tsakanin 15 ga watan Janairu zuwa 20 a kullum sai motoci akalla 532 sun tsallaka zuwa Syria ta mashigar iyakar Hatay.
Sannan a kowace rana tun daga 1 zuwa 5 ga watan, akalla ababen hawa 344 ne suka tsallaka ta sauran iyakin kasar da suka haɗa da Oncupinar da Cobanbey da Karkamis da Akcakale da kuma Ceylanpinar, adadin da ya karu zuwa 484 a kullum tun daga 15 zuwa 20 ga watan.
Bolat ya kuma ƙaryata zargin da ke cewa manyan motocin Turkiyya suna tsallaka zuwa wa yankunan da ke karƙashin ikon 'yan ta'addan ƙungiyar YPG ta hanyar mashigar iyakar Habur.