Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya soki Isra'ila bisa ci gaba da yakar Gaza da "tagwayen barazana" da ke fitowa daga kasar.
"Dukkan duniya na karkashin barazana biyu daga Isra'ila," in ji Altun a ranar Juma'a, inda yake magana kan Isra'ila ke zaluntar masu rauni ta hanyar amfani da matakan diflomasiyya, tattalin arziki, karfin soji ko kuma fasahar kere-kere.
Ya kara da cewa "Masu nuna wariya a yau na amfani da tsari irin na baya a matsayin misali." Ya kuma ce a baya Yahudawa aka zalunta, a yau kuma Musulmai ake zalunta.
Farfagandar masu nuna wariya
Altun ya kuma rawaito Theodor W. Adorno masanin falsafa da zamantakewar dan adam dan kasar Jamus da ke fadin "Farfagandar masu nuna wariya"
Daraktan Sadarwar ya ci gaba da cewa "Adorno wanda shi ma Bayahude ne na Jamus, a littafinsa mai taken 'Antisemitism and Fascist Propaganda' (Kyamar Yahudawa da Farfagandar Masu Nuna Wariya) ya ce farfagandar masu nuna wariya ba makiyanta kawai take danne wa ba, har ma da fatalwa, rauhanai da mutanen boye."
"Yau injinan farfaganda na Isra'ila na amfani da farfagandar masu nuna wariya, kamar yadda Adorno ya fada," in ji Altun.
Altun ya kuma cewa Isra'ila, tare da farfagandar da take yi na "dusashe gaskiya".
Ya kara da cewa "Abin takaici Isra'ila ta kashe 'yan jaridu 64 a hare-haren da take ci gaba da kaiwa."
Batun Kyamar Yahudawa
Altun ya kuma soki batun da ake na kyamar Yahudawa.
"A duk lokacin da ka yi korafi game da manufofin Isra'ila, sai su ce kana nuna kyama ga Yahudawa. Idan ka kare Falasdinawa, sai su ce ba ka amince da wanzuwar kasar Isra'ila ba," in ji Altun, yana magana kan jami'an gwamnatin Isra'ila da ke yawan fakewa da kyamar Yahudawa suna murkushe masu bijire musu.
Daraktan ya kuma bayyana cewa sojojin Isra'ila "Na tura wa kafafen watsa labaran Yammacin Duniya karairayi da kalmomin da za su yi amfani da su" a yayin da suke rawaito yakin."
Altun ya ce kafafen yada labaran "sun fara mayar da Falasdinawa masu laifi sannan suka rika wulakanta su."
"Isra'ila ta bukaci da a kawar da idanu daga wannan dabara tata."
Daraktan ya fadi cewa Isra'ila na kuma jirkita gaskiyar al'amarin ta hanyar farfaganda da barazana guda biyu.
"Rashin nuna muhimmancin karyar da ake yi ne tushen rikicin jirkita gaskiyar" in ji shi, ya kuma ambaci masanin zamantakewa dan kasar Faransa Jean Baudrillard wanda yake cewa duniyar kwaikwayon gaskiya ko wuce gona da iri kan gaskiya sun maye gurbin gaskiyar.
Dubban mutane ne suka gudu zuwa bangaren kudu sakamakon hare-haren da Isra'ila ke kaiwa arewacin Gaza tun 7 ga Oktoba, bayan da Hamas ta kai harin ba-zata a Isra'ila.
A ranar Juma'a, sojojin Isra'ila sun ajiye wasu takardu masu dauke da bayanai a Zirin Gaza da aka mamaye, suna gargadin Falasdinawa da su daina zuwa arewacin Gaza saboda yanki ne na yaki.
A safiyar Juma'ar nan ne aka fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wuta saboda a gudanar da ayyukan jinkai tsakanin sojojin Isra'ila da Hamas har tsawon kwanaki hudu a dukkan yankunan Gaza, za a yi musayar fursunoni da bayar da taimako inda aka dakatar da kai hare-hare.