Erdogan ya ce irin jajircewar da Turkiyya ke yi na kawar da ta'addanci daga tushensa ya sa ƙungiyoyin ta'addanci sun rasa karsashi. / Hoto: AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana bukatar kawo karshen kalubale da hargitsin da Turkiyya ta fuskanta cikin shekaru 150 da suka gabata, musamman a cikin shekaru 50 da suka gabata.

"A cikin shekaru 150 da suka gabata, musamman a cikin rabin karnin da suka gabata, mun sha fama da tashe-tashen hankula. Yanzu lokaci ya yi da za mu ce 'ya isa' da kuma yin ‘sabbin kalamai’," in ji Erdogan a babban taro na 8 na jam'iyyarsa a lardin Diyarbakir

Erdogan ya jaddada hadin kan kasar, yana mai cewa, "Ba za mu bari hadin kan al'ummarmu, da mutuncin kasarmu, da kuma ƙarfin ƙasarmu waɗannan macizan da kunamun su haɗiye su ba," yayin da shugaban yake bayar da misali da wata rubutacciyar waƙa ta Ahmed Arif.

Har ila yau ya bayyana yadda ake ci gaba da yaki da ta’addanci, inda ya yaba da jajircewar da iyaye mata na Diyarbakir suka yi na tsawon shekaru biyar don sake haduwa da ‘ya’yansu da kungiyar ‘yan ta’adda ta PKK ta sace.

"Ta hanyar dabarun mu na kawar da ta'addanci daga tushe, kungiyoyin ta'addanci sun tafka asara ta ɓangaren mayaƙansu da kuma kayan aikinsu," in ji Erdogan.

TRT World