Ma'aikatar Tsaron Turkiyya ta sanar a ranar Litinin cewa, jami'an tsaron kasar sun yi nasarar kashe 'yan ta'addar PKK/YPG 6 a arewacin Iraki da arewacin Siriya.
Ma'aikatar ta bayyana a shafinta na X cewa, an kai wa 'yan ta'addar PKK uku hari a yankin da ake gudanar da ayyukan "Operation Claw-Lock" a arewacin Iraki, inda ta sha alwashin dakarun Turkiyya za su ci gaba da daukar matakan kariya da dakile barna a kan kungiyoyin 'yan ta'adda.
Ta kara da cewa an kai hari kan wasu 'yan ta'adda uku a yankin da ake kira "Operation Peace Spring" a arewacin Siriya.
Ma'aikatar ta ce "Mun kuduri aniyar daƙile ta'addanci daga tushe."
A wani babban ci gaban kuma hukumomin Turkiyya da Siriya sun kama Muhammed Dib Korali a wani samame na hadin gwiwa.
Korali na daya daga cikin wadanda suka kai harin ta'addancin da aka kai a kudancin Turkiyya a shekarar 2013 wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 53.
Gungu mai ƙara faɗaɗa
Mahukuntan Turkiyya na amfani da kalmar ''kawarwa'' wajen nuna cewa 'yan ta'addan da ake magana a kansu sun miƙa wuya ko an kashe su ko kuma an kama su.
'Yan ta'addar PKK na yawan fakewa a arewacin Iraki daga inda suke shirya kai hare-haren wuce gona da iri a Turkiyya.
A shekarar 2022 ne Turkiyya ta kaddamar da ayyukan Operation Claw-Lock domin kai hari kan maboyar 'yan ta'adda a yankunan Metina, Zap, da Avasin-Basyan na arewacin Iraki.
A arewacin Siriya, Ankara ta kaddamar da ayyukan yaki da ta'addanci guda uku tun daga 2016 don hana kafa hanyar ta'addanci da ba da damar samar da zaman lafiya ga mazauna yankin.
A cikin shekaru 40 na ta'addancin da ta ƙaddamar kan Turkiyya, PKK - wadda Turkiyya da Amurka, da EU suka sanya a matsayin kungiyar ta'addanci - ta dauki alhakin mutuwar sama da mutum 40,000, ciki har da mata, yara, da jarirai. YPG reshen PKK ne na Siriya.
'Yan ta'addar PKK/YPG sun nemi yin amfani da rashin tabbas din da ake ciki tun bayan kifar da gwamnatin Assad don cim ma manufofinsu.